Ministan Tinubu Bai Hakura ba, Yana Dakon Sanarwar APC kan Takarar Gwamna
- Jam'iyyar APC ta bayyana Sanata Sharafadeen Alli a matsayin ɗan takararta na gwamnan Oyo a zaɓen 2027
- Alli ya ce nasarar ta dukkan mambobin APC ce, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu da shugabannin jam'iyya, sannan ya buƙaci haɗin kai domin samun nasara
- Tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce har yanzu yana jiran sanarwar hukumance daga shugabancin APC na ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Jam'iyyar APC ta bayyana Sanata Sharafadeen Alli a hukumance a matsayin ɗan takararta na gwamnan Oyo a zaɓen 2027.
Haka kuma ta sanar da Adesoji Adedeji a matsayin mataimakin ɗan takararsa, an gudanar da bikin ƙaddamarwar a Ibadan tare da halartar shugabanni da magoya bayan jam'iyyar.

Source: Twitter
Alwashin da tsohon minista ya yi
Sai dai tsohon Ministan makamashi, Cif Adebayo Adelabu, wanda ya nemi takarar gwamna, ya ce har yanzu yana jiran sanarwar hukumance daga shugabancin APC na ƙasa, cewar Punch.
Alli ya zama ɗan takarar APC bayan ya kayar da Adebayo Adelabu, tsohon mataimakin gwamna Rauf Olaniyan, Akeem Agbaje, Oyedele Alao da sauran masu neman takarar a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar.
A jawabinsa na karɓar takara, Alli ya bayyana cewa nasarar ba tasa kaɗai ba ce, illa ta dukkan mambobin APC masu biyayya.
Ya ce waɗanda suka kada ƙuri'a, matasa, mata da sauran masu ruwa da tsaki duk sun taka muhimmiyar rawa.
Ya ce wannan nasara alama ce ta haɗin kai, juriya, dimokuraɗiyya da ci gaban APC a Oyo, ya ƙara da cewa lokaci ya yi da za a haɗa kai domin gina Oyo mai aminci, wadata da cigaba.
Alli ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa manufofin Renewed Hope suna ƙarfafa 'yan Najeriya wajen farfaɗo da tattalin arziki da ci gaban ƙasa.

Source: Original
Martanin Adelabu kan rasa tikiti
Da yake magana da manema labarai, mai taimaka wa Adebayo Adelabu kan yaɗa labarai, Femi Awogboro, ya ce har yanzu suna jiran hukuncin shugabancin APC na ƙasa.
Awogboro ya ce duk wani ikirari cewa an riga an kammala komai hasashe ne kawai. Ya jaddada cewa kundin tsarin APC ya bai wa shugabancin jam'iyyar na ƙasa ikon sanar da sakamakon ƙarshe.
Ya ƙara da cewa babu wanda ya kamata a ɗauka a matsayin ɗan takara har sai shugabancin APC na ƙasa ya amince da sakamakon, cewar Vanguard.
Awogboro ya buƙaci shugabannin APC su tabbatar da adalci da bin ƙa'ida tun daga farko, ya yi gargadin cewa sulhun da aka gina kan rashin adalci ba zai samar da haɗin kai mai ɗorewa ba.
Ya kuma yi watsi da rahotannin wata jerin sunayen 'yan takara da ake yaɗawa, yana mai cewa ba a san tushenta ba, ya ce dole ne a bi tsarin da ya dace a duk jihohin Najeriya.
Takarar gwamna: Tsohon minista ya tayar da kura
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi magana kan zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a jihar Oyo.
Adebayo Adelabu ya nuna cewa har yanzu uwar jam'iyya ta kasa ba ta sanar da sakamakon zaben ba a hukumance.
Tsohon ministan ya kuma bukaci mambobin jam'iyyar da ka da su fice daga cikinta inda ya nuna cewa hakan bai kamata ba.
Asali: Legit.ng

