'Yan Daba Sun Kai Hari Majalisa ana Shirin Tsige Shugaban Majalisar Dokoki a Najeriya

'Yan Daba Sun Kai Hari Majalisa ana Shirin Tsige Shugaban Majalisar Dokoki a Najeriya

  • Ana zargin wasu ‘yan daba da mamaye harabar Majalisar Dokokin jihar Ondo yayin da ake ci gaba da shirin tsige Kakakin Majalisar, Olamide Oladiji
  • An ruwaito cewa tsagerun ‘yan daban sun fito ne daga Ondo, mazabar Kakakin Majalisar da ake kokarin tsige wa
  • Ma’aikata sun ce lamarin ya jawo tashin hankali sosai kafin ‘yan majalisa da jami’an tsaro su shawo kan matsalar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Ana zargin wasu ‘yan daba da mamaye harabar Majalisar Dokokin Jihar Ondo a safiyar yau Alhamis, yayin da ake ci gaba da shirin tsige Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Olamide Oladiji Landmark.

Majiyoyi daga cikin Majalisar sun ce ‘yan daban sun fito ne daga garin Ondo, wanda shi ne mazabar Kakakin Majalisar da ake fuskantar matsin lambar tsige shi.

Kara karanta wannan

Yan takara 3 da suka sha alwashin dawo da tallafin fetur idan aka zabe su

Olamide Oladiji.
Shugaban Majalisar dokokin jihar Ondo, Rt. Hon. Olamide Oladiji Landmark yana jagorantar zaman majalisa Hoto: Rt. Hon. Oladiji Landmark
Source: Facebook

Me ya faru a Majalisar Ondo?

Daily Trust ta rahoto cewa bayanai sun nuna cewa wasu daga cikin ma’aikatan Majalisar sun ga ‘yan daban suna shiga daga wani ofishi zuwa wani a cikin harabar Majalisar.

An ce lamarin ya jawo fargaba da tashin hankali tsakanin ma’aikata da ‘yan majalisar da ke harabar a lokacin.

Wani ma’aikacin Majalisar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya yi sauki ne bayan wani dan majalisa, Hon. Olajide Oguntodu, da sauran ‘yan majalisar tare da jami’an tsaro sun shiga tsakani.

Ya ce hadin gwiwar ‘yan majalisar da jami’an tsaro ya taimaka wajen fitar da wadanda ake zargin ‘yan daba ne daga harabar Majalisar.

An dawo da zaman lafiyar Majalisa

Majiyar ta ce bayan jami’an tsaro sun shiga lamarin, an samu damar kwantar da hankula tare da dawo da al’amura yadda suke a harabar Majalisar.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da Majalisar ke fuskantar rikicin siyasa da ya shafi shirin tsige Kakakin Majalisar, Olamide Oladiji, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta sake gano lam'a a shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

A halin yanzu, babu karin bayani kan ko an kama wasu daga cikin mutanen da ake zargin sun mamaye harabar Majalisar ko an samu wani rauni sakamakon lamarin.

Ondo.
Harabar Majalisar dokokin jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya Hoto: Oladapo Biola
Source: Facebook

Me ya jawo rikicin tsige Kakakin?

Rahoton ya nuna cewa mamayar harabar Majalisar ta zo ne yayin da ake ci gaba da shirin tsige Kakakin, lamarin da ya kara jawo hankalin jama’a kan rikicin da ke cikin Majalisar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro ko shugabannin Majalisar dokokin kan matakin da za a dauka dangane da lamarin ba.

Kakakin Majalisar Edo ya yi murabus

A wani labarin, kun ji cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo, Rt. Hon Blessing Agbebaku, ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Litinin, 17 ga watan Agusta, 2026.

Bayanai sun nuna cewa Hon. Agbebaku ya dauki matakin sauka daga kujerarsa ne bayan ya samu labarin cewa wasu ‘yan majalisar sun shirya tsige shi.

Jagorancinsa ya fuskanci matsin lamba sosai a watan Mayun 2024 bayan ya dakatar da ‘yan majalisa uku bisa zargin cewa suna shirin tsige shi da sauran manyan jami’an majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262