Sunan Tsohon Gwamna a Kwamitin Kamfe Ya Jawo Matsala, Ƙungiya Ta Yi Barazana ga Tinubu

Sunan Tsohon Gwamna a Kwamitin Kamfe Ya Jawo Matsala, Ƙungiya Ta Yi Barazana ga Tinubu

  • Wata kungiyar da ke goyon bayan sake zaben Bola Tinubu ta yi barazanar janye goyon bayanta kan kwamitin kamfe
  • Ta ce zargin da ake danganta Sheriff da Boko Haram na iya rage karfin gwiwar magoya bayan APC a yankin Arewa maso Gabas
  • Kungiyar ta bukaci shugabancin APC ya sake duba nadin Sheriff, amma ta jaddada cewa har yanzu tana goyon bayan Tinubu da burinsa na sake zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wata kungiyar da ke yakin neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ta yi korafi kan kwamitin kamfe.

Kungiyar ta yi barazanar janye goyon bayanta idan tsohon Gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ci gaba da kasancewa cikin tsarin yakin neman zaben APC.

Kungiya ta taso Ali Modu Sheriff a gaba kan siyasa
Tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff. Hoto: Muhammad Ibrahim Umar.
Source: Facebook

Kungiyar Grassroots Movement for Tinubu Continuity Come 2027 ta bayyana wannan matsayar ne a wata wasika da Punch ta samu.

Kara karanta wannan

Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Sheikh Jingir kan Muslim Muslim

Ana adawa da saka sunan Ali Modu Sheriff

Kungiyar ta ce babban abin da ta ke adawa da shi shi ne nadin Sheriff a matsayin Kodinetan Yakin Neman Zaben APC na Yankin Arewa maso Gabas domin zaben 2027

Shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Sani Ahmad Zangina, ya ce kungiyar na ci gaba da kasancewa mai cikakken goyon bayan sake zaben Tinubu, amma ba za ta iya ci gaba da gudanar da gangamin neman kuri’u ba karkashin wannan tsari.

Zangina ya bayyana cewa damuwar kungiyar ta samo asali ne daga zarge-zargen da aka dade ana yi wa Sheriff kan alakarsa da Boko Haram, yana mai cewa hakan na iya shafar yadda jama’a ke kallonsa da kuma rage amincewar magoya bayan jam’iyyar a yankin.

An bukaci Tinubu ya cire sunan Ali Modu Sheriff
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Zargin da ake yi wa Ali Modu Sheriff

A cewar kungiyar, an taba zargin Sheriff da alaka da kungiyar Boko Haram, kuma sanya shi a wani muhimmin matsayi a yakin neman zaben Shugaban Kasa na iya, a fahimtarta, bata sunan APC da kuma rage kwarin gwiwar masu aikin neman sake zaben Tinubu.

Kara karanta wannan

"Ka shirya barin Aso Villa"; Melaye ya fadi dabarar ADC ta kifar da Tinubu a 2027

Sai dai Ali Modu Sheriff ya sha musanta duk wata alaka ko daukar nauyin Boko Haram, yana mai bayyana zarge-zargen da cewa ba su da tushe.

Zangina ya jaddada cewa kungiyar ba ta cewa an taba samun Sheriff da laifin wata keta doka ba, sai dai ta ce ya kamata a yi la’akari da zarge-zargen tarihi da kuma tasirinsu na siyasa wajen yanke shawarar wanda zai jagoranci yakin neman zaben Shugaban Kasa a Arewa maso Gabas.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan wata kungiyar Nigeria Rescue & Renewal Movement, NRRM, ita ma ta nuna damuwa kan shigar Sheriff cikin tsarin yakin neman zaben APC.

NRRM ta bukaci a sake duba tsarin majalisar yakin neman zaben, tana mai kawo batutuwan gaskiya, rikon amana da kuma amincewar jama’a kan wadanda aka nada shugabannin yakin neman zaben.

APC ta musanta janye kamfen Tinubu

An ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi magana kan rahotannin da ke cewa ta janye jerin sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen.

Sakataren Yaɗa Labarai na APC, Felix Morka, ya ce idan aka samu wani sauyi a jerin sunayen, jam’iyyar za ta sanar da shi yadda ya dace.

Jam’iyyar ta fitar da jerin sunayen ranar Asabar, inda Bola Tinubu da Kashim Shettima suka zama shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.