Bayan Sun Gwabza, Sowore Ya Bayyana Alfarmar da Ya Yi Wa Amaechi

Bayan Sun Gwabza, Sowore Ya Bayyana Alfarmar da Ya Yi Wa Amaechi

  • Omoyele Sowore ya ce ya tuntubi Rotimi Amaechi bayan cacar baki tsakaninsu, inda ya bukaci tsohon gwamnan ya nemi afuwarsa
  • Dan takarar AAC ya ce gwagwarmayarsa ta neman dimokuradiyya ta taimaka wajen samar da tsarin da ya bai wa Amaechi damar rike mukaman gwamnati
  • Sowore ya yi watsi da ra’ayin cewa dole ne dan takarar shugaban kasa ya taba rike mukamin gwamnati kafin ya iya shugabanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore, ya ce ya bukaci Rotimi Amaechi, da ya nemi afuwarsa bayan cacar bakin da ta barke tsakaninsu a taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) na shekara-shekara a Fatakwal.

Sowore ya ce ya yi wannan bukata ne bayan rikicin da ya faru a yayin taron NBA ranar Litinin, 24 ga watan Agustan 2026 yana mai cewa Amaechi ya amfana da dimokuradiyyar da shi ya yi gwagwarmayar ganin an kafa ta.

Kara karanta wannan

Tirkashi: An gwabza tsakanin Sowore da Amaechi a wurin taro

Sowore ya ce ya taimaki Amaechi
Omoyele Sowore da Chibuike Rotimi Amaechi Hoto: @yelesowore, @chibuikeAmaechi
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar Arise News ranar Talata, 25 ga watan Agustan 2026 yayin da yake magana kan abin da ya faru tsakaninsa da tsohon gwamnan.

Sowore ya ce ya tuntubi Amaechi

Sowore ya bayyana cewa bai kamata a auna kwarewarsa ta siyasa kawai da ko ya taba rike mukamin gwamnati ba.

Ya ce dogon lokaci da ya shafe yana gwagwarmayar tabbatar da dimokuradiyya da shugabanci nagari ya taimaka wajen samar da tsarin siyasar da ya bai wa mutane irinsu Amaechi damar shiga gwamnati.

Sowore ya ce bayan taron ya kira Amaechi, inda ya gaya masa cewa ya kamata ya nemi afuwarsa.

“Shi ya sa bayan taron na kira shi na ce masa ya kamata ya nemi afuwata, sai ya ce na zo gidansa mu ci abinci mu sha giya,” in ji Sowore.

Sai dai ya ce ya ki amincewa da gayyatar, inda cikin raha ya ce bai so Amaechi ya sanya masa guba ba saboda yana ganin tsohon gwamnan bai ji dadin abin da ya faru ba.

Kara karanta wannan

Amaechi: Mataimakin Atiku ya bukaci 'yan Najeriya kada su zabi ADC, an ji dalili

Sowore ya ce gwagwarmayarsa ta taimaka wa Amaechi

Sowore ya ce da a ce Najeriya ta ci gaba da kasancewa karkashin mulkin soja, da mutane irin Amaechi ba su samu damar rike manyan mukaman siyasa ba.

Ya ce gwagwarmayar da ya yi wajen ganin an dawo da mulkin dimokuradiyya ta taimaka wajen samar da damar da Amaechi ya samu na shiga siyasa.

“Da ban yi gwagwarmayar dimokuradiyya ba, Rotimi Amaechi ba zai kasance yana tsaye a can jiya ba idan har muna karkashin mulkin soja,” in ji shi.

Ya kara da cewa Amaechi ya samu damar zama kakakin majalisar dokokin jihar Rivers na tsawon shekaru takwas, gwamna na tsawon shekaru takwas, sannan ministan tarayya na tsawon shekaru takwas saboda dawowar dimokuradiyya.

Sowore ya kare kwarewarsa ta shugabanci

Dan takarar na AAC ya ce kwarewarsa ta shugabanci ta samo asali ne daga kishinsa da jajircewarsa wajen neman shugabanci nagari.

Ya bayyana cewa shugabanci ba ya takaita ga wanda ya taba rike mukamin gwamnati kawai, domin ana bukatar mutum mai hangen nesa, manufa da kuma iya hada mutane domin cimma buri.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar APC a Kano ya fadi dalilin goyon bayan Shugaba Tinubu

Sowore ya ce idan ana neman shugaba, ba wai ana neman mutum mai ilimin lissafi ko wani fanni guda kawai ba ne, sai dai wanda ya fahimci fannoni daban-daban kuma zai iya hada kwararru domin gudanar da aiki yadda ya kamata.

Sowore ya yi magana kan rikicinsa da Amaechi
Omoyele Sowore, dan gwagwarmaya a Najeriya Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Sowore zai dawo da tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya bayyana matsayarsa kan dawo da tallafin man fetur.

Omoyele Sowere ya ce zai maido da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng