APC Ta Sake Bude Shafinta, Tana Gayyatar Sababbin Mambobi domin Yin Rijista
- Jam’iyyar APC ta sanar da sake buɗe rajistar zama mamba ta intanet a faɗin Najeriya gabanin zaɓen 2027
- Rajistar za ta shafi tsofaffin mambobi da sababbin masu son shiga jam’iyyar, yayin da tsofaffi za su tabbatar da bayanansu
- APC ta ce ’yan Najeriya masu shekaru 18 ko fiye da haka, waɗanda ke da ingantaccen NIN, za su iya shiga rajistar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar APC, ta sanar da sake buɗe rajistar zama mamba ta hanyar intanet a faɗin Najeriya yayin da ake shirin zaben 2027.
Jam’iyyar mai mulki ta ce za a gudanar da rajistar a dukkan rumfunan zaɓe na ƙasar daga ranar 31 ga Agusta 2026 kuma za ta shafi mambobin da suke ciki da kuma sabbin masu son shiga.

Source: Twitter
Manufar sake bude shafin rijistar APC
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na APC, Felix Morka, ya ce manufar shirin ita ce samar da ingantaccen kundin mambobin jam’iyyar, cewar Punch.
APC ta bayyana cewa mambobin da suke ciki za su tabbatar da bayanansu, yayin da sabbin masu son shiga za su samu damar yin rajistar zama mambobin jam’iyyar.
Morka ya bukaci shugabannin jam’iyya, magoya baya da mambobinta su shiga aikin rajistar, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa tsarin tafiyar da jam’iyyar da shirye-shiryenta.
Ya ce:
“An tsara aikin rajistar ne domin mayar da kundin mambobin jam’iyyar zuwa tsarin zamani na dijital, tabbatar da sahihancin bayanan mambobi, da sauƙaƙa samun bayanan mambobi domin tsare-tsare da yanke shawarar gudanarwa.
“Haka kuma, zai inganta dimokuraɗiyyar cikin gida tare da ƙarfafa ƙudurin jam’iyyar na amfani da sabbin hanyoyin dimokuraɗiyya a Najeriya.”

Source: Twitter
Shawarar APC ga yan Najeriya
APC ta ce ‘yan Najeriya masu shekaru 18 ko fiye da haka, waɗanda ke da ingantaccen Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa, NIN, za su iya yin rajistar zama mambobin jam’iyyar.
Sake buɗe rajistar ya zo ne a lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryensu domin babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan
Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya
APC, wadda ke iko da Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da dama, ta ce ingantaccen kundin mambobi zai taimaka wajen gudanar da harkokin cikin gida, tattara magoya baya da shirya ayyukan jam’iyyar.
Har ila yau, ana sa ran aikin zai bai wa jam’iyyar cikakken bayani kan yawan mambobinta a dukkan rumfunan zaɓe na ƙasar, cewar Daily Post.
Hakan zai taimaka wajen gano kura-kurai da kuma kawar da maimaita bayanan mambobi da ke iya kasancewa sakamakon amfani da kundin rajista na hannu.
Saboda haka, mambobin APC na yanzu za su buƙaci tabbatar da bayanansu, maimakon dogaro da tsohuwar rajistarsu, yayin da sabbin masu shiga za su iya amfani da wannan damar wajen shiga jam’iyyar.
Shugaban APC ya gana da Sanusi II
An ji cewa shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gana da Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II, a fadarsa da ke Kofar Kudu.
Rahotanni sun nuna cews taron ya mayar da hankali kan zaɓen 2027 da ƙoƙarin APC na ƙarfafa matsayinta a siyasar Kano.
Wata majiya ta ce APC na neman goyon bayan fadar sarki da amincewarta ga ‘yan takarar jam’iyyar a Kano.
Asali: Legit.ng
