Zaben 2027: Shugaban APC na Kasa Ya Kwantar da Kai, Ya Roki Alfarmar Sarkin Kano Sanusi II
- Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gana da Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II, a fadarsa da ke Kofar Kudu
- Rahotanni sun nuna cews taron ya mayar da hankali kan zaɓen 2027 da ƙoƙarin APC na ƙarfafa matsayinta a siyasar Kano
- Wata majiya ta ce APC na neman goyon bayan fadar sarki da amincewarta ga ‘yan takarar jam’iyyar a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Shugaban APC na ƙasa, Farfess Nentawe Yilwatda, ya gana da Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II, a jiya Talata, a wani mataki da ake ganin yana da alaƙa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Yilwatda, tare da wasu manyan ‘yan jam’iyyar da shugabannin APC a Kano, ya ziyarci Sarkin Kano a Fadar Kofar Kudu.

Source: Twitter
Vanguard ta ruwaito cewa an gudanar da ganawar ne a cikin sirri kuma ta ɗauki tsawon sa’o’i, yayin da ba a bayyana cikakken abin da aka tattauna ba.
Sai dai wata majiya daga fadar Sarkin ta ce batun zaɓen 2027 da ƙoƙarin APC na ƙarfafa tushenta a Kano na daga cikin abubuwan da aka tattauna.
Me APC ta tattauna da Sanusi?
Majiya ta ce shugabannin APC na ƙasa sun je fadar ne domin neman goyon baya da amincewar basaraken ga dukkan ‘yan takarar jam’iyyar a Kano.
“Shugabannin APC na ƙasa sun zo nan ne domin neman goyon bayan fadar Sarki da amincewarta ga dukkan ‘yan takarar APC a Kano. Sun fahimci yanayin siyasar Kano,” in ji majiyar.
Ta ƙara da cewa APC ta fahimci tasirin da Sarkin Kano ke da shi a tsakanin masu ruwa da tsaki na masarautar da kuma al’ummar jihar, musamman a matakin ƙasa.
Majiyar ta ce jam’iyyar ta kuma san irin tasirin da Sarkin ke da shi wajen wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa fahimtar ‘yan Kano game da haƙƙoƙinsu da mutuncinsu.

Source: Twitter
Me ya sa APC ta je fadar Sarkin Kano?
A cewar majiyar, ziyarar ta kuma nuna yadda jam’iyyar ta fahimci muhimmancin Sarkin Sanusi a yanayin siyasar Kano.
“Ina ganin APC ta fahimci ƙarfi da damar da Sarkin Kano ya nuna a zaɓen da ya gabata, don haka, shugaban APC na ƙasa da shugabannin a jihar suna yin iya ƙoƙarin neman goyon bayan Sanusi II,” in ji majiyar.
Wannan ganawa ta zo ne a daidai lokacin da manyan jam’iyyun siyasa ke ƙara ƙarfafa tsarin su da neman goyon bayan jama’a gabanin babban zaɓen 2027.
Masarautar Kano ta gindaya sharadi
A wani labarin kuma, kun ji cewa masarautar jihar Kano ta wajabta gwajin ƙwaya a matsayin sharadi ga masu neman hawa kujerar sarauta.
Hakimin Dambatta, Dakta Mansur Adnan, ne ya bayyana hakan yayinnwani taron wayar da kai kan illolin shaye-shaye da safarar ƙwayoyi da aka gudanar a fadarsa da ke Dambatta.
Adnan ya ce illolin shaye-shayen ƙwayoyi ne suka sa Masarautar Kano ta buƙaci du wanda ke neman hawa kujerar sarauta ya yi gwajinnƙwayoyi kafin a ba shi sarautar gargajiya.
Asali: Legit.ng

