Jam'iyyar APC Ta Fara Rijistar Mambobinta Miliyan 40 Ta Intanet

Jam'iyyar APC Ta Fara Rijistar Mambobinta Miliyan 40 Ta Intanet

  • Jam'iyyar APC ta fara shirin tunkarar babban zaben 2023, ta ce aiki ya yi nisa na yi wa mutane sama da miliyan 40 rijista ta Intanet
  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya koka kan adadin yawan kuri'un da Tinubu ya samu a zaben shugaban ƙasa 2023
  • Ya ce jam'iyyar karƙashin jagorancinsa zata gudanar da rijista ta na'ura mai kwakwalwa domin tabbatar da yawan ya'yanta

FCT Abuja - Jam'iyya mai mulkin Najeriya APC ta fara shirye-shiryen rijistar mambobinta miliyan 40 ta yanar gizo watau intanet domin tunkarar babban zaɓe na gaba.

Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka yayin da ya karɓi bakuncin wakilan sabbin shugabanni jam'iyyya na ƙasa da mambobin kwamitin zartarwa (NEC).

Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Jam'iyyar APC Ta Fara Rijistar Mambobinta Miliyan 40 Ta Intanet Hoto: OfficialAPCNigeria
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro cewa tawagar wakilan sun ziyarci Ganduje a Sakatariyar jam'iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba, 13 ga watan Satumba, 2023.

Kara karanta wannan

Jerin Ministocin Tinubu Da Kotun Zabe Ta Ayyana a Matsayin Wadanda Suka Lashe Zaben Yan Majalisun Tarayya

Wannan ci gaban na yi wa mambobin APC 'yan Najeriya miliyan 40 rijista ta na'ura na zuwa ne shekaru biyu bayan kwamitin riƙo na Mai Mala Buni ya gudanar makamancin haka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Aikin rijistar mambobin da kwamitin riƙon kwarya na APC karkashin gwamna Mala Buni ya gudanar wancan lokacin, ya nuna 'yan Najeriya sama da miliyan 40 ne mambobin jam'iyar.

Meyasa APC ta ɗauki wannan matakin?

Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, Ganduje ya bayyana cewa, manufar yin rajistar na’ura mai kwakwalwa shi ne don tattara bayanan karfin jam’iyyar a halin yanzu.

Shugaban APC na kasa ya koka kan sakamakon zaben shugaban kasa na 2023, yana mai jaddada cewa yawan kuri’un da jam’iyyar ta samu ya yi nesa da irin yawan ‘ya’yanta da suka yi wa rajista.

Kara karanta wannan

Ahaf: Rashin Gaskiya Ta Sa Kotu Ta Tsige Dan Majalisar NNPP a Kano, An Ba Dan Takarar APC

A rahoton jaridar Within Najeriya, Ganduje ya ce:

"Idan za ku iya tunawa, muna da mambobi miliyan 41. Amma a lokacin zaben shugaban kasa, kuri'a miliyan takwas kaɗai muka samu. Me ya faru da sauran?."
"Wannan shine dalilin da ya sa muke buƙatar zama dijital domin mu tabbatar da cewa muna aiki da sahihan bayanai. Wani mataki da muka dauka yanzu shi ne muna nazarin yin rajista ta na'ura."
"An riga an fara aikin. Ya kamata ku kasance cikin shirin cewa duk membobinmu za a yi musu rajista ta intanet don mu sami ainihin adadi na gaskiya."

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi Ya Fice Daga PDP Zuwa APC a Abuja

A wani rahoton kuma Yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Kogi, jam'iyyar APC ta yi babban kamu daga babbar jam'iyyar adawa PDP.

Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba wa tsohon mataimakin gwamna bisa sauya sheƙar da ya yi zuwa APC.

Kara karanta wannan

Al’ummar Yarbawa Sun Yi Wa Kwankwaso Da Gwamnatin Kano Addu’a Ta Musamman

Asali: Legit.ng

Online view pixel