Masarautar Kano Ta Bi Zamani, Ta Kafa Sabon Sharadi ga duk Mai So a Nada Shi Sarauta
- Masarautar jihar Kano ta wajabta gwajin ƙwaya a matsayin sharadi ga masu neman hawa kujerar sarauta
- Hakimin Dambatta ya ce matakin ya zama dole saboda illolin da shaye-shayen miyagun kqwayoyi ke haifarwa a rayuwar mutum da ta al’umma
- Hukumar NDLEA ta buƙaci sarakuna da iyaye su taimaka wajen yaƙi da safarar ƙwayoyi musamman tsakanin matasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Masarautar Kano ta sanya yin gwajin ƙwayoyi a matsayin ɗaya daga cikin sharuɗɗan da duk wanda ke neman hawa kujerar gargajiya a masarautar zai cika.
Hakimin Dambatta, Dakta Mansur Adnan, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai kan illolin shaye-shaye da safarar ƙwayoyi da aka gudanar a fadarsa da ke Dambatta ranar Asabar.

Source: Twitter
Dalilin wajabta gwajin kwaya a Kano
Ya ce matakin ya zama dole ne saboda illolin da shaye-shayen ƙwayoyi ke haifarwa ga mutane da al’umma baki ɗaya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
2027: ADC ta fito da bayani, an ji dalilin Atiku na ƙin sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya
Adnan ya ce illolin shaye-shayen ƙwayoyi ne suka sa Masarautar Kano ta buƙaci du wanda ke neman hawa kujerar sarauta ya yi gwajin ƙwayoyi kafin a ba shi sarautar gargajiya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron ya haɗa hakimai da dagatai daga ƙaramar hukumar Dambatta domin wayar da kansu kan haɗarin shaye-shaye da safarar ƙwayoyi.
Hukumar NDLEA ta nemi haɗin kai
Kwamandan NDLEA na shiyyar Dambatta, Zailani Muhammad, ya ce babban burin hukumar shi ne yaƙi da shaye-shaye da safarar ƙwayoyi domin kare rayuka da makomar al’umma.
Muhammad ya buƙaci sarakunan gargajiya da mazauna yankin su ba hukumar haɗin kai ta hanyar kai rahoton masu safarar ƙwayoyi da wuraren da matasa ke saye ko shan haramtattun ƙwayoyi.
Ya ce hukumar a shirye take ta karɓi rahotanni, shawarwari da koke-koke da suka shafi yaƙi da shaye-shaye da safarar ƙwayoyi.

Source: Facebook
Kwamandan ya ce samun nasara a yaƙi da matsalar na buƙatar haɗin gwiwar gwamnati, sarakunan gargajiya, iyaye, malamai da sauran al’umma.
Muhammad ya kuma wayar da kan mahalarta taron kan illolin shaye-shaye, abubuwan da kan jefa matasa cikin shan ƙwayoyi da kuma alamomin da ya kamata iyaye su kula da su.
Ya nuna wasu daga cikin ƙwayoyin da matasa suka fi amfani da su tare da bayyana illolinsu, kamar yadda Daily Post ta rahoto.
Da gaske Sarkin Kano ya fadi jarabawa?
A wani rahoton, kun ji cewa jami’ar Northwest ta Kano (NWUK) ta musanta wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ke dauke da ikirarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya faɗi wasu darussa.
Jami’ar ta bayyana bidiyon da rubuce-rubucen da aka danganta da shi a matsayin ƙarya, marasa tushe kuma na yaudara, tana mai cewa babu wata hujja da ke tabbatar da zargin da ake yadawa.
NWUK ta kuma bukaci daukacin al’ummar jami’ar da sauran jama’a da su yi watsi da bidiyon, rubuce-rubucen da kuma duk wasu ikirarin da suka samo asali daga bayanan.
Asali: Legit.ng
