Natasha: Matar Fitaccen Mawaki Ta Ce Wata Rana Za Ta Zama Shugabar Kasa a Najeriya
- Hon. Natasha Osawaru, matar fitaccen mawakin Najeriya 2Baba, ta bayyana burinta na zama shugabar Najeriya a nan gaba
- ’Yar majalisar dokokin jihar Edo ta yi wannan furucin ne yayin bikin cikar kakanta Gabriel Igbinedion shekaru 92 a duniya a Benin City
- Natasha ta ce za ta yi aiki tukuru wajen gina siyasarta domin ta zama shugabar Najeriya tun kafin kakanta ya rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - Natasha Osawaru, matar fitaccen mawakin Najeriya Innocent Idibia, wanda aka fi sani da 2Baba, ta bayyana burinta na zama shugabar Najeriya wata rana.
Natasha Osawaru, wadda mamba ce a Majalisar Dokokin Jihar Edo, ta bayyana hakan ne yayin bikin cikar kakanta, Gabriel Igbinedion, shekaru 92 a Benin City, jihar Edo.

Source: Instagram
Yar majalisa ta yabawa kakanta
Daily Trust ta ruwaito cewa a yayin bikin, Natasha Osawaru ta yi wa Igbinedion yabo sosai, inda cikin kauna ta kira shi “abin kaunarta”, tare da bayyana farin cikinta da yadda yake kara girma cikin shekaru.

Kara karanta wannan
Ana cikin wahala a ƙasa, Atiku, Tinubu sun kwashi miliyoyin dala sun kashe a Amurka
Ta kuma yi wa kakanta alkawarin cewa za ta yi aiki tukuru domin ta zama shugabar Najeriya tun yana raye.
“Kai abin mamaki ne, a yanzu kamar masoyi na kake, ina sonka sosai. Yayin da kake kara shekaru, sai ka kara dadi da kyau, abin mamaki ne kasancewa tare da kai kaka.
"Na yi maka alkawarin cewa zan zama shugabar wannan kasa kafin ka tafi,” in ji ta.
An yada bidiyon kalaman Natasha
An yada wani bidiyo da ke nuna ’yar majalisar tana furta kalaman a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar kakanta, inda bidiyon ya yadu sosai a kafafen sada zumunta.
Natasha Osawaru tana wakiltar mazabar Egor a Majalisar Dokokin Jihar Edo, kuma a baya-bayan nan aka nada ta shugabar marasa rinjaye a majalisar.
Bayan nadin nata, ta bayyana cewa mukamin ya wuce matsayin siyasa kawai, domin a ganinta amana ce aka dora mata.
Burin siyasar Natasha Osawaru

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An shiga cikin gida an kashe babban malamin Najeriya a ƙasar waje
Burin siyasar Natasha Osawaru ya zo ne a daidai lokacin da shahararta ke kara habaka, duka a matsayinta na ’yar majalisar jiha da kuma matar 2Baba.
Ta auri mawakin a watan Yulin 2025, watanni kadan bayan rabuwar da aka yi ta yadawa sosai tsakanin 2Baba da tsohuwar matarsa, Annie Macaulay Idibia.

Source: Facebook
Auren ya jawo hankalin jama’a sosai, musamman saboda yanayin rabuwar 2Baba da Annie, kamar yadda Vangaurd ta kawo.
Sai dai mawakin ya sha yin watsi da ikirarin cewa Natasha Osawaru ce ta haddasa rugujewar aurensa na baya, yana mai cewa ba ita ce sanadin rabuwarsa da Annie ba.
Kakakin Majalisar Edo ya yi murabus
A wani labarin, kun ji cewa Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo, Rt. Hon Blessing Agbebaku, ya yi murabus daga mukaminsa bayan gano abin da aka shiryam masa.
Bayanai sun nuna cewa Hon. Agbebaku ya dauki matakin sauka daga kujerarsa ne bayan wasu ‘yan majalisar sun shirya tsige shi.
Agbebaku, wanda ke wakiltar mazaɓar Owan West, an zaɓe shi a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Edo ta Takwas a watan Yunin 2023.
Asali: Legit.ng