Zaɓen 2027 Akwai Kallo, Masu Ruwa da Tsakin PDP, ADC Sun Goyi bayan Tinubu

Zaɓen 2027 Akwai Kallo, Masu Ruwa da Tsakin PDP, ADC Sun Goyi bayan Tinubu

  • Masu ruwa da tsaki na PDP, NDC da APC a mazabar sanatan Ikot Ekpene sun amince da Tinubu, Akpabio da Eno a zaɓen 2027
  • Sun ce sun yanke shawarar ne bayan nazarin siyasar ƙasa da Akwa Ibom, tare da duba irin gudunmawa da ayyukan shugabannin uku
  • Akpabio ya ce goyon bayan ya nuna haɗin kan jihar, yana mai tabbatar da cewa za su bai wa Tinubu da Eno kashi 100 cikin 100

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Uyo, Akwa Ibom - A ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026, masu ruwa da tsaki na jam’iyyun PDP, NDC da APC sun gana a Akwa Ibom.

Masu ruwa da tsakin sun amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Gwamna Umo Eno domin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Maganar Wike ka iya son tabbata, gefen Atiku,Obi sun magantu kan yiwuwar hadaka

Tinubu ya samu goyon bayan ƴan ADC, PDP
Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a taro. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

An bayyana ƙudurin ne cikin wata sanarwa da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Ukanafun/Oruk Anam, Hon. Unyime Idem, ya karanta, cewar The Nation.

Musabbabin goyon bayan Tinubu

An bayyana cewa amincewar ta biyo bayan wani taron masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na mazabar sanatan, inda suka tattauna halin siyasar ƙasa da jihar.

Masu ruwa da tsakin sun amince baki ɗaya da goyon bayan Tinubu domin ya sake komawa wa’adi na biyu a matsayin shugaban ƙasa, Akpabio domin ci gaba da wakiltar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma a Majalisar Dattawa, sannan Eno domin ya sake tsayawa takarar gwamna.

An amince da ƙudurin ne bayan wani ƙuduri da Sanata Emmanuel Ibokessien ya gabatar, wanda Hon. Iboro Ekanem ya mara wa baya.

Masu ruwa da tsakin sun ce sun yanke shawarar ne bayan nazarin halin siyasar ƙasar da jihar, tare da tantance irin gudunmawa da ayyukan shugabannin uku.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 6, malaman addini 500 sun bayyana dan takarar shugaban kasarsu a 2027

Tinubu, Akpabio ya samu goyon bayan ƴan adawa
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Facebook

Da yake jawabi bayan amincewar, Akpabio ya danganta matakin da yanayin zaman lafiya da ake samu a Akwa Ibom, yana cewa jam’iyyun adawa sun haɗa kai wajen goyon bayan Tinubu, Eno da shi.

Akpabio ya ce amincewar ta nuna haɗin kai a jihar, musamman a mazabar sanatan Akwa Ibom North-West, yana mai bayyana irin goyon bayan da aka samu.

Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma yi kira ga ‘yan siyasar jihar da su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da sulhu yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Ya lura da halartar shugaban PDP na Akwa Ibom, Hon. Aniekan Akpan, da wasu ‘yan takarar Majalisar Dokoki ta Ƙasa na jam’iyyun adawa a taron, cewar Punch.

Akpabio ya bayyana halartar tasu a matsayin alamar samun fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasa a jihar, yana mai kira ga kowa da ya ci gaba da zaman lafiya.

An yaba Tinubu kan saka Matawalle a kamfe

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa Nyesom Wike bai zama darakta janar na kamfen Tinubu ba'

An ji cewa Ma’aikatar Tsaro ta yaba da naɗin Bello Matawalle a cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu na 2027.

Ma’aikatar ta ce naɗin ya nuna amincewar Tinubu da ƙwarewar Matawalle wajen gudanar da harkokin gwamnati.

Matawalle ya gode wa Tinubu da shugabannin APC, tare da yin alƙawarin amfani da ƙwarewarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.