Hankalin Kasashen Ya Tashi da Korea Ta Arewa Ta Yi Gwajin Makami Mai Linzami
- Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami zuwa teku, bayan Koriya ta Kudu ta bukaci ta ba da hakuri kan nakiyoyin da suka jikkata sojoji uku
- Makamin ya tashi daga Wonsan da misalin 6:30 na safe, inda ya yi tafiyar sama da kilomita 700 kafin ya fado cikin teku
- Kim Yo-jong, 'yar'uwar Kim Jong-un, ta yi watsi da bukatar neman afuwa, tana mai cewa Pyongyang a shirye take don duk wani mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Korea ta Arewa ta harba wani makami mai linzami zuwa teku ranar Asabar, bayan ta yi watsi da zargin Koriya ta Kudu kan nakiyoyi da suka jikkata sojojinta.
Sojojin Koriya ta Kudu sun ce makamin ya tashi daga yankin Wonsan da misalin 6:30 na safe, inda ya yi tafiyar kilomita 700 zuwa Tekun Gabas.

Source: Getty Images
Jami'an tsaron teku na Japan sun ce makamin na iya kasancewa mai linzami, kuma da alama ya fada cikin teku, yayin da suka gargadi jiragen ruwa, cewar The Guardian.
Sojojin Koriya ta Kudu sun kara sanya ido kan yiwuwar wasu gwaje-gwajen makamai, tare da raba bayanan sirri da Amurka da Japan.
Ofishin shugaban kasar Koriya ta Kudu ya gudanar da taron gaggawa na kwamitin tsaron kasa domin nazarin harin da Pyongyang ta kai.
Kim Yo-jong, 'yar'uwar shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un, ta yi watsi da bukatar Seoul na neman afuwa kan nakiyoyin.
Koriya ta Kudu ta ce nakiyoyin Koriya ta Arewa ne suka haddasa fashewar da ta jikkata sojojin kasar uku a yankin da aka haramta sojoji.
Shugaban Koriya ta Kudu Lee Jae Myung ya bukaci Pyongyang ta koma tattaunawa, duk da bukatar sojojin kasar na neman afuwa kan lamarin.
Sai dai Kim Yo-jong ta soki wannan mataki, inda ta bayyana Seoul a matsayin abin kyama tare da yin watsi da tayin tattaunawar.
Ta kuma gargadi Koriya ta Kudu cewa Pyongyang a shirye take ta fuskanci duk wani mataki da Seoul za ta dauka kan fashewar nakiyar.
Wani masani kan harkokin Koriya ta Arewa, Cheong Seong-chang, ya ce harba makamin na iya kasancewa kokarin Pyongyang na samun martanin Seoul.
Ya kuma ce akwai yiwuwar Koriya ta Arewa ta yi gwajin wani sabon nau'in makami mai linzami a wannan harin.
Koriya ta Arewa ta gudanar da gwaje-gwajen makamai masu linzami sama da sau 10 cikin shekarar 2026, wasu kuma bayan ta yi Allah-wadai da atisayen sojojin Seoul da Washington.
A shekarun baya, Pyongyang ta kara tsaurara matsayinta kan Koriya ta Kudu, inda ta yi watsi da hadin kan kasashen biyu tare da bayyana Seoul a matsayin babban makiyi.
Korea ta Arewa ta yi wa Amurka barazana
A baya, an ji cewa Korea ta Arewa ta yi gargadin ɗaukar matakan kai hari kan abokan gaba bayan isowar jirgin yaƙin ruwan Amurka Koriya ta Kudu.
Rahoto ya ce barazanar ta zo ne kwana guda bayan Koriya Ta Arewa ta harba makamin roka mai gajeren zango zuwa cikin teku.
Kasar ta zargi Amurka da Korea Ta Kudu da haɗa kai wajen haɗa makaman nukiliya da na wasu kayan yaki don tsoratar da ita.
Asali: Legit.ng

