Magana Ta Fito: An Samu Bayanai kan Makarantun Firamare da Sakandare da Tinubu Ya Halarta
- An samu bayanai kan makarantun firamare da sakandare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara gudanar da karatunsa
- Makarantar da ke kan titin Palm Street a Aroloya ta fara aiki ne a shekarar 1857, kuma daga baya ta samu ginin hawa uku
- Bayan kammala karatun firamare, Tinubu ya zarce Children Home School a Ibadan kafin daga bisani ya yi karatu a Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT Abuja - Wani tarihin rayuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ofishin Jakadancin Najeriya ya wallafa ya bayyana makarantar firamare da sakandaren da ya halarta.
Tarihin rayuwar na Tinubu da aka wallafa ya kuma bayyana wasu bayanai kan karatunsa da aikinsa.

Source: Getty Images
Bola Tinubu ya fara karatu Legas
A cewar takardar, Shugaba Tinubu ya fara karatun firamare a St. John’s Primary School Aroloya da ke Legas.
An kafa makarantar ne a shekarar 1857 a cikin wata ƙaramin rumfa da ke cikin harabar coci, kafin daga bisani ta ci gaba da faɗaɗa.
Zuwa shekarar 1870, makarantar ta samu wani gini mai siffar harafin T, sannan daga baya aka kammala ginin hawa uku a ranar 28 ga Satumba, 1954.
Ministan ilimi na gwamnatin tarayya a lokacin ne ya ƙaddamar da sabon ginin makarantar.
A ranar 11 ga Oktoba, 1954, malamai da ɗalibai suka koma sabon ginin a hukumance, wanda har yanzu yake kan wannan wurin.
Fitattun mutane sun halarci makarantar
An ce fitattun ’yan Najeriya da dama sun yi karatu a wannan makaranta, lamarin da ya sanya ta zama ɗaya daga cikin muhimman makarantu a tarihin ilimi a Lagos.
Bayan kammala karatun firamare, tarihin rayuwar da aka wallafa ya nuna cewa Tinubu ya zarce Children Home School da ke Ibadan.
Makarantar firamaren da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya halarta tana lamba 30, Palm Street, Aroloya, Lagos Island, Legas. Ana iya tuntuɓar makarantar ta lambar waya +2348064804573.

Kara karanta wannan
2027: Yan takarar gwamna a Kano da jihohi 6 sun ɗauki matsaya kan dawo da tallafin fetur
Karatun Tinubu a Amurka
Tinubu ya yi karatun digiri a Amurka, inda ya fara a Richard J. Daley College da ke Chicago, sannan ya zarce zuwa Chicago State University.
Ya kammala karatunsa a shekarar 1979 da digirin Bachelor of Science (BSc) a fannin lissafin kuɗi.
Shugaba Tinubu ya yi aiki a matsayin akanta a wasu kamfanonin Amurka da suka haɗa da Arthur Andersen, Deloitte da GTE Services Corporation.
Bayan komawarsa Najeriya a shekarar 1983, ya shiga Mobil Oil Nigeria, inda daga baya ya zama babban jami’in kamfanin.
Tinubu ya shiga siyasa
An ce tafiyar Tinubu a siyasa ta fara ne a shekarar 1991, lokacin da ya shiga jam'iuyar Social Democratic Party (SDP).
A shekarar 1992, an zaɓe shi zuwa Majalisar Dattawa, inda ya wakilci mazabar Legas ta Yamma a Jamhuriyar Najeriya ta Uku wadda ba ta daɗe ba.
Bayan soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993, Bola Ahmed Tinubu ya zama ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa National Democratic Coalition, wata ƙungiyar rajin tabbatar da dimokuraɗiyya.
Ƙungiyar ta tattara goyon baya domin dawo da mulkin dimokuraɗiyya tare da amincewa da Moshood Abiola a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni.

Source: UGC
Sanata Yari ya yabi Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Abdulaziz Yari, ya ce babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya kai Shugaba Bola Ahmed Tinubu nagarta.
Sanata Yari ya ce duka yan takarar da ke ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 ba su kai shi cancanta da ƙwarewa ba.
Asali: Legit.ng

