Da na sani ban yiwa yan bindiga afuwa a baya ba, Gwamna Aminu Masari

Da na sani ban yiwa yan bindiga afuwa a baya ba, Gwamna Aminu Masari

  • Gwamna Masari yace sulhu da yan bindiga bai amfanar da komai ba
  • Masari ya bayyana koma bayan farko da aka samu yayin sulhu
  • Gwamnatin jihar Katsina ta kafa sabbin dokoki don kawo karshen yan bindiga

Abuja - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce bisa abubuwan da yan bindiga ke yi da kuma bayanan da yake samu, da ya sani bai yi sulhu da yan bindiga a baya.

Gwamnan a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar ChannelsTV, yace dukkan afuwan da suka yiwa yan bindiga a shekarun baya bai haifar da wani sakamakon kwarai ba.

A cewarsa, bai yi nadamar hakan ba amma an samu koma baya sosai ga shirin afuwa da sulhu da yan bindigan.

Yace:

"Ba na nadama, amma abinda nike fadi shine da na san hakan zai kasance da ban yi ba. Saboda a lokacin da muka fara a 2016, akwai shugabannin yan bindigan amma an kashe dukkansu, wannan shine koma baya na farko."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki 6 hannunsu, yan bindiga sun saki yayan sakataren jihar Katsina

"Na biyu da mukayi bayan zaben 2019 ma an samu koma baya. Mun yi kokari amma kuma mukayi la'akari cewa, 'wai da wa muke magana?' Ba wani addini suke wa yaki ba. Kawai tsageru ne, kuma barayi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da na sani ban yiwa yan bindiga afuwa a baya ba, Gwamna Aminu Masari
Da na sani ban yiwa yan bindiga afuwa a baya ba, Gwamna Aminu Masari Hoto: Katsina State
Asali: Twitter

Gwamnan Katsina ya haramta sana'ar cajin waya a jiharsa

Cikin yunkurin kawo karshen matsalar tsaro, Gwamnan jihar Katsina, Malam Aminu Bello Masari, ya haramta sana'ar cajin waya a kananan hukumomi 18 cikin 34 na jihar.

Masari ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin rantsar da kwamitin da aka kafa don tabbatar da ana biyayya ga sabbin dokoki 10 da gwamnatin jihar tayi.

An rantsar da kwamitin ne a gidan gwamnatin jihar dake birnin Katsina

Masari na ganin cewa wannan sabon doka na hana sana'ar cajin waya a wadannan kananan hukumomi zai taimaka wajen rage matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Bamu yi sulhu da Fulani ba: Yan Irigwe da akewa zargin kashe matafiya a Jos

Bayan kwanaki 6 hannunsu, yan bindiga sun saki yayan sakataren jihar Katsina

A bangare guda, Kabir Muhammad, Yayan sakataren gwamnatin jihar Katsina, Muhammad Inuwa, da aka sace ranar Larabar da ta gabata, ya samu yanci bayan kwanaki shida.

Mai magana da yawun Inuwa, Kabir Yar'adua, ya tabbatar da hakan ranar Talata, rahoton Punch.

Yace:

"Lallai an saki dattijon amma babu kudin da aka biya na fansa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel