Katsina: Sakataren Gwamnati, Mustapha Inuwa ya yi murabus daga kan muƙaminsa

Katsina: Sakataren Gwamnati, Mustapha Inuwa ya yi murabus daga kan muƙaminsa

  • Sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, ya yi murabus daga kujerarsa, zai nemi takarar gwamna a 2023
  • A wata sanarwa da Ofishinsa ya fitar, Inuwa ya gode wa gwamna Aminu Masari bisa damar da ya ba shi ta aiki tun 2015
  • Tuni dai gwamna Masari ya amince da murabus ɗinsa kuma ya masa fatan alkairi a harkokin da ya sa a gaba

Katsina - Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa, ya yi murabus daga kan muƙaminsa a yunkurin da yake na gaje kujerar gwamna Aminu Bello Masari.

Inuwa, wanda ya jima da ayyana shiga tseren takarar gwamnan Katsina a 2023 ƙarƙashin APC, mafi yawan mutane na ganin babban ƙusa ne kuma zai iya lallasa sauran yan takara.

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Jam'iyyar APC ta faɗi gaskiyar abinda ya sa ta sanya kuɗin Fom Miliyan N100m

Ya ɗauki matakin aje muƙaminsa ne domin biyayya ga tanade-tanaden dokoki dake cikin kundin dokokin zaɓe 2022.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina ya aje aiki.
Katsina: Sakataren Gwamnati, Mustapha Inuwa ya yi murabus daga kan muƙaminsa Hoto: Mustapha Inuwa TV/facebook
Asali: Facebook

A takardar murabus mai ɗauke da sa hannun SSG, kuma Legit.ng ta gani, Inuwa ya ce ya ɗauki matakin ne domin maida hankali kan harkokin siyasarsa da takara da ya sa gaba.

Takardan wacce ta kai kan teburin Mai girma gwamna Masari, Inuwa ya nuna tsantsar godiyarsa da gatan da gwamna ya masa na aiki a matsayin SSG tun 2015.

A takardan wacce Legit.ng Hausa ta gani, Inuwa ya ce:

"Ina Addu'a Allah ya kara karfafa tare da kare mai girma gwamna a siraɗin karshe na mulkinsa zango ma biyu, Allah ya sa duk kokarin da kake yi ka samu nasara."

Shin gwamna Masari ya amince da matakin?

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya karyata Buhari baro-baro, ya ce an fi samun zaman lafiya a mulkin Jonathan

A nasa bangaren, Gwamna Aminu Masari, ya amince da murabus ɗin SGG, kuma ya masa fatan Alheri a harkokin siyasar da ya sa gaba.

A takardan amincewa da murabus ɗin, Masari, ya yaba wa SSG bisa sadaukarwan da ya yi na aiki a gwamnatinsa tun daga 2015 zuwa 15 ga watan Afrilu.

Legit.ng Hausa ta zanta da wani mazaunin Katsina kuma dan amutun Mustapha Inuwa, ya tabbatar da lamarin aje aikin mai gidansa.

A cewar matashin ɗan siyasan:

"Eh, mai gida ya aje aikinsa kuma ba tun yau ba, idan ka duba takardan ta kai mako ɗaya. Ya yi haka ne domin maida hankali wajen neman kujerar gwamna a wurin mai ba da mulki."

Wakilin mu ya tambayi Aliyu Idris cewa shin ya suke ji raɗe-rafin da mutane ke yaɗawa cewa tsohon SSG na da hannu a matsalar tsaron Katsina, ya ce:

"Wannan siyasa ce kawai, kuma Me gida ya gama magana tun da ya ce, idan shi ne alkairi ga mutanen Katsina Allah ya ba shi."

Kara karanta wannan

Na hannun daman Ganduje ya canza shawara, ya janye daga takarar gwamnan Kano a 2023

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya fusata, ya umarci Hafsoshin tsaro su ceto mutanen da yan bindiga suka sace

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nuna damuwarsa kan karuwar matsalar tsaro a faɗin kasa yayin taronsa da Hafsoshin tsaro.

Cikin gaggawa kuma ba tare da bata lokaci ba, Buhari ya umarci su ceto dukkan mutanen da yan ta'adda ke tsare da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel