Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce

Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce

- Hotunan wasu kasaitattun gidajen wasu 'yan kabilar Ibo sun yi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani

- Wani saurayi ne ya wallafa hotunan katafaren gidajen a shafinsa na Twitter inda yace gidansu ne na Anambra

- Jama'a da dama sun yi ta yarda da cewa lallai akwai mashahuran masu kudi a Najeriya, kuma ko a dan aiki ka zauna a gidan, ka caba

Kasaitattun hotunan wani gida dake jihar Anambra ya karade kafafen sada zumuntar zamani, wanda mutane suka yi ta cewa lallai akwai 'yan kabilar Ibo masu dukiyar gaske.

Wadannan hotunan sun janyo cece-kuce da musu iri-iri.

An ce katafaren gidan a jihar Anambra yake, bayan nan ne wani saurayi ya wallafa wasu hotunan wani gida mai kama da wancan, inda yace hotunan gidansu yana ta yawo.

KU KARANTA: Da duminsa: Allah ya yi wa kwamishinan cikin gida na jihar Sokoto rasuwa

Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce
Duba katafaren gidajen da aka gina a kauyen nan da yadda suka janyo cece-kuce. Hoto daga @yungruffad
Source: Twitter

Wannan cece-kucen na yanar gizo ya nuna cewa akwai masu kudin da mujallun Forbes da Bloomberg ba dole a ce suna duba wasu yankuna ba.

KU KARANTA: Hotuna: 'Aljanun Kano' da suka dade suna damfara sun shiga hannun hukuma a Katsina

A wani labari na daban, 'yan sandan jihar Bauchi sun kama wani matashi mai shekaru 19, wanda aka fi sani da Sara-Suka, bisa laifin shirya liyafar lalata da holewa a karamar hukumar Dass dake jihar.

Yayin da 'yan sandan hedkwatar Yan doka dake babban birnin jihar suka fita sintiri a ranar Laraba, kwamishinan 'yan sandan, CP Lawan Tanko Jimeta ya ce wadanda ake zargin sun addabi al'umma da hatsabibanci da kwacen wayoyi.

Ba anan kadai suka tsaya ba, ana zarginsu da shirya wata liyafa, wacce ake zargin ta holewa da lalata ce a garin Dass a ranar 11 ga watan Janairu, The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel