Kakakin majalisar dokokin jihar APC ya shiga matsala, da yiwuwar a tsige shi daga muƙamin

Kakakin majalisar dokokin jihar APC ya shiga matsala, da yiwuwar a tsige shi daga muƙamin

  • Shugaban majalisar dokokin Ondo na fuskantar barazanar tsige shi daga muƙaminsa kan kalaman da ya yi na goyon bayan Gwamna
  • Honorabul Olamide Oladiji ya yi ikirarin cewa ƴan majalisa 18 sun amince za su goyi bayan takarar gwamna mai-ci a inuwar APC mai mulki
  • Amma 13 daga cikin ƴan majalisar sun musanta kalaman shugabansu kana suka kaɗa kuri'ar rashin amincewa da jagorancinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Olamide Oladiji, ya jefa kansa cikin matsala bayan ya yi ikirarin ƴan majalisa 18 na tare da takarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Oladiji ya samu halartar wurin da Gwamna Aiyedatiwa ya ayyana kudirinsa na neman tikitin takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan Ondo mai zuwa a 2024.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da wasu manyan ƙusoshin APC sun fara shirin kafa sabuwar jam'iyya domin tunkarar Tinubu

Kakakin majalisar Ondo, Olamide Oladiji.
Yan majalisa 13 sun kada kuri'ar rashin amincewa da shugaban majalisar Ondo Hoto: Hon. Olamide Oladiji
Asali: Twitter

Kakakin majalisar ya marawa Aiyedatiwa baya

Da yake jawabi a wurin, kakakin majalisar ya yi iƙirarin cewa mambobi 18 na majalisar dokoki na goyon bayan burin gwamnan, The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Mambobin majalisar dokokin jihar Ondo 18 sun amince su marawa Aiyedatiwa baya. Hatta waɗanda ba ƴan APC ba ne suna tare da mu kuma da ikon Allah za mu kai ga nasara.

Ƴan majalisa sun kaɗa kuri'ar rashin amincewa

Amma a wata sanarwa, ‘yan majalisa 13 sun yi watsi da ikirarin da kakakin majalisar ya yi na cewa suna goyon bayan Gwamna Lucky Aiyedatiwa a matsayin dan takarar APC.

A cewarsu, ikirarin da ya yi ba gaskiya bane, yaudara ce kuma ya saɓawa ƙa'idojin majalisa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Daga nan sai mambobin majalisar suka kaɗa kuri'ar rashin amincewa da kakakin majalisar dokokin, inda suka ce babu inda majalisa ta amince da goyon bayan Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta ɗauki sabon mataki a shirinta na tsige mataimakin gwamna, ta faɗi muhimmin dalili 1

Wani sashin sanarwar ta ce:

"Shugaban majalisa ba shi da hurumi a dokance na ayyana goyon bayan wani ɗan takarar gwamna a madadin majalisar dokoki ba tare da amincewar mambobi ba.
"Bisa haka ne mu ka kada kuri'ar rashin amincewa da shugabancin kakakin majalisar, Honorabul Olamide Oladiji.
"Majalisar na ƙara jaddada aniyar ta na bin doka da oda da kuma tabbatar da gaskiya a duk matakin da za ta ɗauka da zai amfani al'ummar Ondo."

Abin da ya sa PDP ta rasa jihar Ondo

A wani rahoton kuma Gwamna Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta faɗi zaben gwamnan jihar Ondo a 2020 ne saboda rashin haɗin kai da rarrabuwar kawuna.

Seyi Makinde ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar reshen jihar Ondo da ƴan kwamitin NWC na ƙasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel