Gwamnan Sokoto Ya Gayawa Mutane Abin da Za su Yi a Kawo Karshen 'Yan Bindiga
- Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto ya mika bukatarsa ga jama'a kan hanyar da za a magance 'yan bindiga
- Mai girma gwamnan ya ce gwamnatinsa ta bai wa jami’an tsaro motoci masu sulke 62, da motocin sintiri sama da 200 da babura 2,000 domin yaki da ‘yan bindiga
- Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci al’ummar jihar Sokoto su goyi bayan takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya kalubalanci mazauna jihar da su taimaka wajen tona asirin masu ba ‘yan bindiga bayanai daga cikin al’umma domin dakile hare-haren ‘yan bindiga.
A halin yanzu, jihar Sokoto na cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga masu yawa.

Kara karanta wannan
Jami'an tsaro sun yi wa 'yan bindiga rubdugu a Katsina yayin dakile mummunan shirinsu

Source: Facebook
Gwamnati na tallafa wa tsaro
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Aliyu ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 19 ga watan Agustan 2026 a karamar hukumar Bodinga ta jihar, yayin kaddamar da sayar da kayan abinci a farashi mai rahusa.
Ya ce gwamnatinsa na ci gaba da bai wa hukumomin tsaro tallafi domin kawo karshen matsalar ‘yan bindiga masu dauke da makamai.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta yi iya bakin kokarinta wajen tallafa wa jami’an tsaro, inda ya kawo misalin samar da motoci masu sulke 62 a baya-bayan nan.
Ya kara da cewa an kuma bai wa jami’an tsaron sama da motocin sintiri 200 da babura 2,000 domin inganta ayyukansu da yaki da ‘yan bindiga a jihar.
Wace bukata Gwamna Aliyu ya nema?
“Muna bukatar mu fahimci cewa magance matsalar rashin tsaro na bukatar hadin kanmu, don haka dole ne mu taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da suka dace."
“Haka kuma dole ne mu tona asirin masu ba da bayanai da ke zaune a cikinmu, domin su ne ke bai wa ‘yan bindiga bayanai kan abubuwan da ke faruwa a yankunan karkara,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma roki al’ummar jihar da su ci gaba da yin addu’o’i sosai domin kawo karshen rashin tsaro a jihar da ma Najeriya baki daya.

Source: Original
Gwamnan Sokoto ya goyi bayan Tinubu
A karshen jawabinsa, Aliyu ya bukaci al’ummar jihar da su yi watsi da abin da ya kira kamfen na bata suna da ake yi wa Tinubu. Ya kuma bukaci mutanen jihar su goyi bayan takarar Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.
Ahmad Aliyu ya kara tabbatar wa Shugaba Tinubu cewa gwamnatinsa za ta ba shi cikakken goyon baya wajen neman sake lashe zaben shugaban kasa a 2027.
'Yan bindiga sun kashe mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari Unguwar Aminu da ke Kandarawa, a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kashe mutane biyu, suka sace wasu mutane shida tare da jikkata huɗu da harbin bindiga a daren Talata, 11 ga watan Agustan 2026.
Asali: Legit.ng
