Abu Ya Girma: Za a Shiga Kasuwa, Shago Shago domin Nema wa Tinubu Ƙuri'u

Abu Ya Girma: Za a Shiga Kasuwa, Shago Shago domin Nema wa Tinubu Ƙuri'u

  • Kungiyar RHGN mai goyon bayan Shugaba Bola Tinubu ta kaddamar da yakin neman goyon baya na musamman
  • Mazi Franklin Ngoforo ya ce za su rika shiga shaguna suna bayyana yadda manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu suka shafi kasuwanci
  • RHGN ta ce tana fadada shirinta a Kudu maso Gabas ta hanyar kasuwanni, makarantu da cibiyoyin addini domin kara samun goyon bayan Tinubu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Aba, Abia - Kungiyar masu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu mai suna Renewed Hope for Greater Nigeria (RHGN) ta shirya ƙaddamar da kamfe na musamman.

Kungiyar za ta kaddamar da yakin neman goyon baya na "Kasuwa zuwa Kasuwa" a Kudu maso Gabas domin tara goyon baya gabanin babban zaben 2027.

An fara nema wa Tinubu a kasuwa, za a bi shago shago
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

An ƙaddamar da kamfen Tinubu a kasuwa

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

An kaddamar da shirin ne a Kasuwar Ariaria da ke Aba a Abia tare da halartar 'yan kasuwa, masu shigo da kayayyaki da shugabannin kasuwa, cewar Punch.

Mataimakin shugaban RHGN na Kudu maso Gabas, Mazi Franklin Ngoforo, ya ce shirin zai rika isa ga 'yan kasuwa daga shago zuwa shago domin bayyana tasirin manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.

Ya bayyana cewa manufar shirin ita ce tabbatar da cewa 'yan kasuwa sun fahimci yadda sabbin sauye-sauyen tattalin arziki ke shafar kasuwancinsu da hanyoyin samun abin rayuwa.

Ngoforo ya ce hade kasuwar musayar kudaden waje ya kawo karshen tsarin da wasu masu alaka da gwamnati ke samun kudaden waje cikin sauki kafin su sake sayarwa.

Ya ce wannan manufa ta saukaka samun kudaden waje ga 'yan kasuwa da masu shigo da kaya, musamman a Kudu maso Gabas inda kasuwanci ke taka muhimmiyar rawa.

Ya kuma danganta ayyukan ci gaba da ake yi a Abia da sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin tarayya, yana mai cewa karin kudaden shiga ya taimaka wajen aiwatar da ayyuka.

Ngoforo ya bukaci 'yan kasuwa su mara wa Shugaba Tinubu baya a kokarinsa na sake neman wa'adi a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Ya ce sakon ya kamata ya isa kowane bangare na kasuwar domin 'yan kasuwa su fahimci yadda manufofin tattalin arzikin kasa ke tasiri ga harkokinsu na yau da kullum.

An ƙaddamar da kamfen ɗin Tinubu a Abia
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Twitter

Shugaban kungiyar ya yi alƙawari ga Tinubu

Da yake jawabi bayan rantsar da shi, shugaban reshen RHGN na Kasuwar Ariaria, Cif Clifford Igbokwe wanda aka fi sani da Ogbuefi Mbaukwu, ya gode wa shugabannin kungiyar.

Ya yi alkawarin cika nauyin da aka dora masa, yana mai cewa kaddamar da reshen kasuwar wani bangare ne na fadada ayyukan RHGN a Kudu maso Gabas, cewar Tribune.

A cewarsa, kungiyar ta riga ta kaddamar da kungiyoyi biyu a Owerri tare da gudanar da shirin wayar da kan limaman Pentecostal a Awka.

Ya kara da cewa kafa reshen kasuwanni zai kara fadada dabarun kungiyar a kasuwanni, makarantu da cibiyoyin addini domin kara samun goyon bayan Tinubu kafin zaben 2027.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne tare da halartar dimbin 'yan kasuwa, masu shigo da kaya da shugabannin Kasuwar Ariaria, daya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Afirka ta Yamma.

Tinubu ya kaddamar da tallafi ga talakawa

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hango abin da zai hana Tinubu cin zaɓe, ya ba shi mafita

Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin an kawar da matsanancin talauci a fadin Najeriya.

Ya ce sama da Dala biliyan uku za a kashe ta sabbin shirye-shiryen tallafawa manoma, 'yan kasuwa, 'yan gudun hijira da bangarorin lafiya da ilimi.

Gwamnatin tarayya ta ce ta riga ta tallafa wa gidaje miliyan 15 masu karamin karfi, lamarin da ya taimaka wajen fitar da mutum miliyan 7.5 daga talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.