"Musulunci Ya Yi Rashi," Sarkin Musulmi Ya Shiga Alhini bisa Rasuwar Sarki Mai Martaba a Najeriya

"Musulunci Ya Yi Rashi," Sarkin Musulmi Ya Shiga Alhini bisa Rasuwar Sarki Mai Martaba a Najeriya

  • Sarkin Musulmi ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwar Mai martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON
  • Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce raasuwar basaraken babban rashi ne ga masarautar Gumel, Jigawa da daukacin al'ummar Musulmi
  • Ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya karbi kyawawan ayyukansa, Ya saka masa da gidan Aljannah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi jimamin rasuwar Sarkin Gumel da ke jihar Jigawa, Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON.

Sarkin Gumel ya rasu ne ranar Alhamis, 3 ga watan Satumban 2026, a birnin Alkahira na kasar Masar, bayan shafe shekaru 46 a kan karagar mulki.

Sarkin Musulmi.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Sarkin Musulmi ya mika sakon ta'aziyya

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Sanatoci sun shiga damuwa da manyan sarakuna 2 suka rasu a Arewa

Vangaurd ta rahoto cewa Sarkin Musulmin ya yi jimamin wannan rashsi a cikin sakon ta’aziyyar da Bashir Adefaka ya sanya wa hannu a madadin tawagar yada labaransa kuma aka fitar ranar Juma’a.

Sultan ya bayyana marigayi Sarkin Gumel a matsayin fitaccen malami, taskar hikima kuma uba ga kowa.

Ya ce rasuwar marigayin babban rashi ne ga Masarautar Gumel, jihar Jigawa, sarakunan gargajiya da kuma al’ummar Musulmi baki daya.

Sarkin Musulmi ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Gumel, gwamnatin da al’ummar jihar Jigawa, Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa da daukacin al’ummar Musulmi.

Sultan ya ce musulmi sun yi rashi

Ya ce marigayi Sarkin Gumel ya gudanar da nauyin da ke kansa na karagar mulki cikin mutunci, tawali’u da jajircewa, yana mai cewa shekaru 46 da ya shafe yana mulki sun zama wani babban tarihi ga masarautar.

Sarkin Musulmi ya ce:

“Marigayi Sarkin ya kasance malami, mutum mai hikima kuma uba ga kowa. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’ummarsa hidima tare da inganta zaman lafiya, ilimi da kuma kare kyawawan al’adunmu da dabi’unmu na gargajiya.”

Kara karanta wannan

Yadda aka yi jana'izar Sarkin Gumel cikin jimami, Kashim da manyan kasa sun halarta

Ya kara da cewa sarakunan gargajiya za su yi kewar hikimarsa, shawarwarinsa da kuma halinsa na uba, tare da irin gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban al’umma.

Sarkin Musulmin ya bukaci al’ummar Masarautar Gumel daJigawa su tsaya tsayin daka wajen imani da addu’a, tare da ci gaba da riko da dabi’un zaman lafiya, hadin kai, mutunci da yi wa jama’a hidima da marigayin Sarkin ya shahara a kansu.

Gumel.
Mai martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmed Muhammad Sani II, CON Hoto: Masarautar Gumel
Source: Facebook

Sarkin Musulmi ya yi wa marigayin addu'a

Ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya karbi kyawawan ayyukansa, Ya saka masa da alherin shekarun da ya shafe yana yi wa al’umma hidima, tare da ba shi Aljannatul Firdaus.

Sarkin Musulmin ya kuma yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalan marigayin, Majalisar Masarautar Gumel da daukacin al’ummar jihar Jigawa hakuri da juriyar jure wannan babban rashi.

Gwamna Namadi ya yi ta'aziyya

Kun ji cewa Gwamna Umar Namadi ya bayyana rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji Dr Ahmed Muhammad Sani II, a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa.

Ya ce marigayi Sarkin ya kasance babban shugaban gargajiya mai kima, wanda ya sadaukar da shekaru 45 na rayuwarsa wajen yi wa al'ummarsa hidima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262