Zargin El Rufai: Hadimin Uba Sani Ya Kare Janar Christopher Musa

Zargin El Rufai: Hadimin Uba Sani Ya Kare Janar Christopher Musa

  • Babban mai ba Gwamnan Kaduna Uba Sani shawara kan harkokin jama’a, Victor Bobai, ya kare Ministan Tsaro Christopher Musa kan kalamansa game da El-Rufai
  • Bobai ya ce bai dace a fassara kalaman Musa a matsayin suka ko siyasa kan tsohon gwamnan na jihar Kaduna ba
  • Ya bukaci masu suka su mayar da martani da hujjoji da shaidu, maimakon cin mutunci ko kai hari kan ministan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Babban mai ba Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani shawara kan harkokin jama’a, Victor Mathew Bobai, ya kare Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), kan kalamansa game da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Bobai ya ce bai dace a fassara kalaman Janar Musa da ya yi yayin wata hira tattaunawa ba a matsayin hari na kashin kai ko kuma siyasa kan El-Rufai ba..

Kara karanta wannan

‘Mulkinsa ya shafi kowa a Kaduna': Jigon APC ya kare kalaman minista kan El Rufai

Janar Musa ya yi kalamai kan El Rufai
Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa Hoto: Ministry of Defence Nigeria
Source: Twitter

Bobai ya bukaci a mayar da martani da hujjoji

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Bobai ya bukaci mutanen da ba su amince da yadda ministan ya tantance abubuwan da suka faru a Kaduna ba su duba batutuwan da ya gabatar, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Ya ce ya kamata su mayar da martani da hujjoji da sahihan bayanai, maimakon kai wa Musa hari na kashin kai.

“Dole ne mu bambanta tsakanin umarnin hukuma da ra’ayin siyasa. Janar Musa bai bayar da wani umarnin soja ba, bai sanar da wata manufar tsaro ba, kuma bai umurci Rundunar Sojin Najeriya ta goyi bayan wata jam’iyyar siyasa ba,” in ji shi.

Ya ce Janar Musa na da damar magana

Bobai ya ce ya fahimci nauyin da ke kan ofishin da Musa ke rike da shi, amma ya ce hakan bai hana jami’an gwamnati shiga tattaunawar al’amuran da suka shafi ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Siyasar 2027: Abba Kabir Yusuf zai karfafi 'yan Kannywoo

Ya bukaci masu sukar ministan da su kalubalanci bayanansa da hujjoji idan suna ganin ba su da inganci.

“Ku kalubalanci hujjojin Janar Musa idan ba ku amince da su ba. Ku gabatar da shaidu. Ku gyara shi inda ya dace. Amma kada ku maye gurbin muhawara da zagi,” in ji Bobai.

Ya tuna da tarihin aikin Janar Musa

Mai taimaka wa gwamnan ya kuma yi nuni da tarihin aikin soja na Musa, yana mai cewa ya rike manyan mukaman kwamanda daban-daban kafin daga bisani ya zama Shugaban Hafsoshin Tsaro sannan Ministan Tsaro.

“Wannan mutum ne wanda rayuwarsa ta ƙwarewa ta kasance kan hidimar tutar Najeriya tun kafin kowace jam’iyyar siyasa ta zama mai muhimmanci ga matsayinsa na yanzu,” in ji shi.

Ya nemi a binciki kalaman El-Rufai

Dangane da batutuwan da Janar Musa ya taso game da gwamnatin El-Rufai, Bobai ya bukaci ’yan jarida da masu sharhi su duba jawaban tsohon gwamnan, hirarrakinsa da sauran kalamansa na bainar jama’a.

Ya ce batutuwan da ministan ya tattauna sun kasance cikin muhawarar jama’a a Kaduna tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Shugaban da ya nemi mata su kashe aurensu kan zaben APC ya magantu

Saboda haka, ya bukaci kafafen yaɗa labarai su dogara da cikakkun faifan bidiyo da bayanan da za a iya tabbatar da sahihancinsu yayin rahoto.

Janar Musa ya yi zarge zarge kan El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: Bello El-Rufai
Source: Facebook

ICPC ta kori jami'i kan matar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta kori wani jami’in tsaro a dalilin tirka-tirkar da ake yi da Malam Nasir El-Rufai.

Hukumar ICPC ta sallami wannan ma’aikaci ne saboda ya ba Aichatou Assabe El-Rufai damar ganin Malam Nasir El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng