Wuta Ta Yi Wuta: Iran Ta Kai Hari Mai Zafi kan Jiragen Yakin Amurka

Wuta Ta Yi Wuta: Iran Ta Kai Hari Mai Zafi kan Jiragen Yakin Amurka

  • Rundunar IRGC ta Iran ta ce ta harba makamai masu linzami kan wani jirgin ɗaukar jiragen yaƙi da jirgin yaki na Amurka
  • Iran ta yi zargin cewa jiragen ruwan Amurkan suna tsangwamar jiragen Iran tare da shiga aikin killace tashoshin ruwan kasar
  • Wani masani a Tehran ya ce takunkumi da killace tashoshin ruwan da Amurka ke yi na jefa Iran cikin matsanancin hali, amma ƙasar na shirin mayar da martani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran – Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta harba “makamai masu linzami da dama” kan wani jirgin ɗaukar jiragen yaƙin Amurka da wani jirgin ruwan yaki.

IRGC ta bayyana cewa ta kai harin ne saboda jiragen ruwan Amurkan suna tsangwamar jiragen Iran tare da shiga aikin killace tashoshin ruwan kasar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Jirgin yaƙi na sojoji ya yi hatsari, ya faɗo kusa da dandazon taron mutane

Iran ta harba makamai kan jiragen Amurka
Makami mai linzami na Iran da aka harba Hoto: @Araghchi
Source: Twitter

Iran ta ce jiragen Amurka sun gudu

Tashar Aljazeera ta ce kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa IRGC ta yi ikirarin cewa jiragen ruwan biyu sun samu lahani sakamakon harin.

A cewar rundunar, jiragen sun fuskanci ƙarin barazanar hare-hare, lamarin da ya tilasta musu barin yankin da ake gwabzawa.

IRGC ta kuma yi tsokaci kan wata sanarwar baya-bayan nan daga Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM.

Kwamandan CENTCOM, Brad Cooper, ya ce idan Iran ta kai hari kan jiragen ruwan Amurka guda biyu, Amurka za ta ɗora mata ƙarin tsadar tattalin arziki ta hanyar kai hari kan jiragen ruwanta guda uku.

IRGC ta yi barazanar mayar da martani

Rundunar ta ce idan Amurka ta ci gaba da abin da ta kira ayyukan ƙiyayya da tsokana, ya kamata gwamnatin Amurka ta shirya fuskantar gagarumar amsa daga dakarun Iran.

Ta ƙara da cewa ƙarfin sojojin Iran ya fi na baya, tana mai cewa: “Mun fi ƙarfi fiye da kowane lokaci.”

Kara karanta wannan

Amurka ta kaddamar da sababbin hare hare kan jirgin Iran

Sai dai bayanan da IRGC ta bayar game da lalacewar jiragen ruwan Amurka da tilasta musu tserewa ba su samu tabbaci mai zaman kansa a cikin rahoton ba.

Masani ya ce Iran ba za ta yi shiru ba

Ali Akbar Dareini, wani masani a Cibiyar Nazarin Dabarun Tehran, ya ce hare-haren Amurka kan jiragen dakon man fetur na Iran babban batu ne da ƙasar ba za ta iya barin shi ba tare da mayar da martani ba.

Dareini ya bayyana cewa hare-haren ba lallai su tilasta Iran mika wuya ba, sai dai suna iya ƙara mata ƙwarin gwiwar mayar da martani mai tsanani.

Iran ta kai wa Amurka hari
Samfurin makamai masu linzami na Iran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Killace tashoshin ruwa na ƙara matsin lamba

A cewarsa, takunkuman tattalin arziki da kuma killace tashoshin ruwan da Amurka ta kakaba wa Iran na haifar da matsanancin ciwo ga tattalin arzikin ƙasar.

Duk da haka, Dareini ya ce Iran tana da tsare-tsaren da take shiryawa domin tunkarar wannan matsin lamba.

“Iran ba za ta iya jure wa ci gaba da wannan killace tashoshin ruwan ba, don haka tuni take shirin karya hakan,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Yadda Rasha ke taimakon Iran wajen hada makamai masu linzami

Ya kuma yi ikirarin cewa Iran na da wasu tsare-tsare da za su iya haifar da tashin farashin man fetur a duniya zuwa sama da dala 100 kan kowace ganga.

Amurka ta famaki jirgin Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Wani jirgin ruwan dakon man fetur na Iran ya fuskanci hari daga sojojin Amurka kusa da yankin tashar jiragen ruwa na tsibirin Kharg da ke mashigar tekun Gulf.

Rahotanni sun ce jirgin ruwan dakon man fetur din ya fuskanci harin ne a yankin da ake ajiye jiragen ruwa a kusa da tsibirin

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng