‘Mahaddacin Kur’ani ne’: Dan APC Ya Fadi Makarantar da Tinubu Ya Yi a Borno

‘Mahaddacin Kur’ani ne’: Dan APC Ya Fadi Makarantar da Tinubu Ya Yi a Borno

  • Wani ɗan siyasa daga Bauchi ya ce Bola Ahmed Tinubu cikakken Musulmi ne kuma mahaddacin Alƙur'ani, yana mai ƙaryata masu sukar addininsa
  • Dan siyasar ya yi iƙirarin cewa Tinubu ya yi haddar Alƙur'ani a Maiduguri, yana mai kira ga jama'a su tambayi mutanen garin domin tabbatarwa
  • Ya kuma bukaci a riƙa zaɓar nagartattun mutane daga kowace jam'iyya, yana yabawa masu goyon bayan Tinubu ciki har da Dr. Bala Wunti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Wani dan siyasa a jihar Bauchi kuma masoyin Bola Tinubu ya yi magana game da soyayyarsa ga shugaban kasa.

Mutumin mai suna Malan Dan Malan daga jihar Bauchi ya caccaki masu sukar Bola Tinubu game da Musuluncinsa a Najeriya.

Masoyin Tinubu ya ce shugaban kasa mahaddaci ne
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Dan Malan ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya yi hira da tashar Zamani TV wanda ta wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya hango abin da zai hana Tinubu cin zaɓe, ya ba shi mafita

An gano inda Tinubu ya haddace Kur'ani

Dan siyasar ya bayyana cewa Bola Tinubu cikakken Musulmi ne sabanin yadda wasu ke yada karairayi game da addininsa saboda kawai siyasa.

Ya ce ya san inda Bola Tinubu ya haddace Kur'ani mai girma inda ya ce shugaban kasar mahaddacin Kur'ani ne tun tuni.

Ya ce:

"Yanzu ga daya daga cikin alherin Bola Tinubu, wallahi tallahi na farko cikakken Musulmi ne, kuma mahaddacin Kur'ani ne.
"Mahaddacin Kur'ani ne, a Maiduguri ya yi haddar Kur'aninsa, duk wadanda suke zaginsa kaza-kasa to gashi Allah ya gwadawa mutane.
"A zawirar Gwani Modu Gwani Kolo ya yi karatu, kuma ka je ka tambayi 'yan Maiduguri, ni Ahmad Bola Tinubu na ke yi."
An yabawa salon mulkin Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Malan Dan Malan zai yi shinkafa da wake

Malan Dan Malan ya ce ya kamata mutane su gane cewa ana bukatar dauko mutanen kirki a siyasa ko daga wace jam'iyya ya fito.

Ya ce ko meye za a fada a fada amma shi Bola Ahmed Tinubu ya ke yi inda ya ce duk inda wani dan takara mai kyau yake zai bi shi idan yana da cancanta.

Kara karanta wannan

ADC ta fadi yadda za ta kawo karshen mulkin Tinubu a 2027

"Babu yadda za ka yi ka dauko dan APC ka ce shi kadai za a yi, ko ka dauko dan PRP ko ADC ka ce shi kadai za a yi.
"Dole mutane suna bukatar dauko a nan da can, duk inda mutanen kirki suke ka dauko a hada da na hannunka.
'Duk wanda yake tafiyar Tinubu tun daga kan Bala Wunti da saura, duk muna yi masu godiya, sabosa duk matsalar da ake samu an dinke ta idan dai a kan Bola Tinubu ne."

- Malan Dan Malan

An shawarci Tinubu game da Wunti

An ji cewa wanda ya nemi takarar gwamnan Bauchi a karkashin APC, Bala Mai Jama'a Wunti na ci gaba da samun goyon bayan matasa.

Wani matashi mai suna Ahmad Gamji ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ba Dr. Bala Wunti babban mukami saboda gogewa da ƙwarewarsa.

Ya ce basira, gogewa da karɓuwar Dr. Bala Wunti a wajen jama'a sun sa ya cancanci jagoranci domin bunƙasa harkar mai da tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.