Mutane Sun Kone Kurmus da Motar Gas Ta Fashe a Kusa da Sojoji
- Rahotanni sun nuna cewa wata motar gas fashe a wani wajen da sojoji suka kafa shinge a kan babbar hanyar Abuja-Lokoja a jihar Kogi
- Gobara ta kama motocin da suka dauko kaya guda uku kuma direbobi da mataimakan su sun kone, adadin wadanda suka rasa rai ya kai shida
- Bayanan da Legit ta samu sun nuna cewa an kai gawar wadanda suka mutu asibiti bayan da jami'an tsaro suka kai dauki a wajen da abin ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi - An yi babban hadari a daren Talata bayan da mota mai dauke da tunkuyar gas ta tashi wuta tana kusa da wani shingen soji a kan babbar hanyar da ta hada birnin Abuja da Lokoja a jihar Kogi, inda mutane shida suka rasa rayukansu.
Bala'in ya auku a ƙarƙashin yankin da sojoji ke aiki a Chikara, ya kuma haifar da zuwan gaggawa daga jami'an 'yan sanda, da sauran hukumomi domin kai dauki.

Source: Getty Images
Rahoton da jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewa bayan jami'an 'yan sanda, jami'an hukumar tsaro da ke lura da kan hanya, wato FRSC ma sun hallara wajen da gaggawa.
Yadda hadarin gas ya faru
Wani mutum da ya ga abin da ya faru da idanunsa ya shaida wa manema labarai yadda lamarin ya gudana, daga farko zuwa karshe.
Ya bayyana cewa nan take motar ta kama da wuta yayin da ta nufi shingen da sojoji suka kafa, bayan haka gobara ta bazu ta kai motocin da ke kusa da ita.
Rahoton Business Day ya nuna cewa matukin motar da ke dauke da gas din da mataimakinsa na cikin wadanda suka rasu nan take.
Motocin da suka kone a wajen
Haka kuma gobara ta kama motoci masu ɗauke da kaya guda uku kuma direban kowannen su da mataimaki sun mutu a cikin wutar. Adadin wadanda suka rasa rai a wannan bala'i ya kai shida.
Motocin da aka ƙone sun fito ne daga jihohi daban-daban, inda aka ga rajistar su sun fito ne daga jihar Jigawa, jihar Legas da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Bayan lamarin, jami'an tsaro sun kai gawarwakin wadanda suka mutu Babban Asibitin Abaji domin a kai a ajiye su. Sannan an dauke motocin da aka kona daga kan hanya domin a ba da damar zirga-zirga.

Source: Original
Jami'an 'yan sanda na jihar Kogi ba su yi bayani game da lamarin ba, domin mai magana da yawunsu, ASP Salisu Oyiza Afusat, bai amsa kira ko sakon rubutu da aka aika masa ba har zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari.
Gobara ta kona coci a Gombe
A wani labarin, mun kawo muku cewa gobara ta tashi a wani cocin ECWA a jihar Gombe, inda ta kona kayayyakin da suke da darajar miliyoyin Naira.
Hukumar kashe gobara ta tarayya ta bayyana cewa ta kai dauki a lokacin da wutar ta tashi, kuma jami'anta sun yi kokari wajen ganin an kashe wutar.
Kamfanin Halima Factor da ke jihar Gombe ya fitar da sanarwar jaje game da abin da ya faru, inda ya yi fatan Allah ya kiyaye faruwar haka a gaba.
Asali: Legit.ng

