"Ko Ka Yi Murabus"; Peter Obi Ya ba Tinubu Zabi 2 kan Rashin Tsaro

"Ko Ka Yi Murabus"; Peter Obi Ya ba Tinubu Zabi 2 kan Rashin Tsaro

  • Peter Obi da ke neman takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NDc a zaben, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsao
  • Dan takarar wanda ya ziyara jihar Oyo, ya nuna damuwa kan har yanzu daliban da ak. Sace ci gaba da zama a hannun 'yan bindiga
  • Ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus saboda gaza sauke nauyin da ke kansa na samar da tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Dan takarar shugaban kasa jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro a karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Peter Obi ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya yi murabus ko kuma ya janye duk wani shiri na neman sake tsayawa takara.

Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus
Peter Obi tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @PeterObi, @aonanuga1956
Source: Facebook

Obi ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 6 ga watan Yulin 2026 a shafinsa na X, biyo bayan ziyarar da ya kai wa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya sake bukatar Tinubu ya yi murabus kan badakalar da IMF ta tono

Ya kai ziyarar ne don jajantawa kan ci gaba da tsare daliban da aka sace sama da kwanaki 50 da suka gabata a jihar Oyo.

Obi ya ce gwamnatin Tinubu ta gaza

Peter Obi ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza magance matsalar rashin tsaro da ke kara ta'azzara a kasar, da kuma nuna abin da ya bayyana a matsayin rashin nuna tausayi ga wadanda abin ya shafa.

A cewarsa, sakamakon rashin shugabanci nagari yana kara fitowa fili a fadin kasar nan. Ya nuna juyayinsa ga gwamnati da al'ummar jihar Oyo, yana mai cewa suna da kowane dalili na jin takaici kan ci gaba da tsare yaran da aka yi garkuwa da su.

Ya kara da cewa ya yi amfani da taron domin bayyana kwarewarsa a matsayin gwamnan jihar Anambra wajen tunkarar kalubalen tsaro, inda ya tuno irin goyon bayan da shugabannin baya suka bai wa gwamnonin jihohi a lokutan rashin tsaro.

Ya yi mamaki kan Tinubu

A cewarsa, ya yi mamakin jin cewa wai Tinubu bai tuntubi Gwamna Makinde ba game da sace yaran.

Kara karanta wannan

Dan takarar sanata ya yi wa APC gardama kan batun sauya sunan shi

“A yayin taronmu na tsawon sa'o'i biyu, na bayyana kwarewata wajen magance rashin tsaro a matsayina na gwamnan jihar Anambra. Na tuna yadda Shugaba Olusegun Obasanjo, sannan daga baya Shugabanni Umaru Musa Yar’Adua da Goodluck Jonathan suke kiran mu da kansu sau da yawa duk lokacin da muka fuskanci manyan kalubalen tsaro."

- Peter Obi

Wane zabi Obi ya ba Tinubu kan rashin tsaro?

Ya zargi gwamnatin yanzu da rashin kwarewa da kuma tausayin da ake bukata domin magance kalubalen kasar. Don haka, ya bukaci Tinubu da ya yi murabus domin maslahar kasa.

“Lamarin ya nuna rashin kwarewa da rashin tausayi gaba daya, wanda aka hada shi da rashin nuna rashin damuwa a fili."
"Ya kamata shugaban kasa ya yi murabus ko kuma, a kalla, ya kaurace wa neman sake tsayawa takara domin maslahar kasarmu. Wannan kira na kishin kasa ne, ba na siyasa ba. Sabuwar Najeriya mai yiwuwa ce."

- Peter Obi

Obi ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa kan rashin tsaro
Peter Obi na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

An bukaci Peter Obi ya biya N50bn

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi na neman shiga matsala kan wasu kalamai da ya yi kan mataimakin shugaban jam'iyyar LP na kasa, Abayomi Ararambi.

Abayomi Ararambi ya yi zargin cewa kalaman na Peter Obi sun taba kimarsa tare da bata masa suna a siyasance.

Ararambi ya bukaci Obi ya janye maganarsa a fili, ya ba shi hakuri, sannan ya biya shi Naira biliyan 50 a matsayin diyyar zargin kalaman batanci da ya yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng