Da Gaske Tinubu, Ministocinsa Sun Manta Sun Rera Tsohon Taken Najeriya? Gaskiya Ta Fito
- An yi ta yada wasu rahotanni cewa Shugaba Bola Tinubu da ministoci sun rera tsohon taken Najeriya a taro
- Rahotannin da ake yaɗawa sun jawo maganganu a kafofin sadarwa inda yan Najeriya ke sukar shugabannin
- An yi binciken kwa-kwaf domin gano gaskiyar lamarin tare da yin amfani da dabaru na tantance dadewar bidiyon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Yan Najeriya da dama sun caccaki Shugaba Bola Tinubu da ministocinsa kan 'rera' tsohon taken kasar.
An yada wani rahoto cewa Tinubu da ministocinsa sun rera tsohon taken Najeriya yayin taron a birnin Abuja.

Source: Twitter
Sai dai TheCableCheck ya karyata ikirarin da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa tsohon bidiyo ne.
Bidiyon da ake yadawa kan Tinubu, ministocinsa
A bidiyon, an nuna Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ministocinsa suna rera tsohon taken Najeriya wanda aka ce sabon bidiyo ne.
Masu yada bidiyon sun yi ikirarin cewa an samu rudani yayin rera taken wanda ya dauki hankulan mutane.
A ranar 29 ga Mayu, 2024, Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar dawo da tsohuwar wakar kasa mai taken "Nigeria, We Hail Thee."
Kafin hakan, Najeriya tana amfani da wakar "Arise, O Compatriots" tun daga shekarar 1978.
A cikin bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta, Tinubu da ministocinsa suna rera wakar "Arise, O Compatriots", ba sabuwar wakar kasa "Nigeria, We Hail Thee" da ake amfani da ita yanzu ba.
Wani mai amfani da dandalin X mai suna @CrownprinceCom2 ya wallafa bidiyon tare da ikirarin cewa ya nuna Tinubu da ministoci suna rera tsohuwar wakar kasa a wani taro. Wallafar ta samu martani da yawa, tare da dubban masu kallo da hulda.
Shafin Politics Nigeria ma ya wallafa bidiyon a Facebook tare da taken cewa an samu rudani yayin da Tinubu da ministocinsa suka rera tsohuwar wakar kasa.

Source: UGC
Binciken da aka gudanar kan rade-radin

Kara karanta wannan
Kiristocin Arewa sun tsoma baki kan kisan da aka yi wa malamar Islamiyya a Kaduna
Sai dai batun da ke cikin bidiyon ya shafi kare matakin cire Hukumar Babban Birnin Tarayya, FCTA, daga tsarin TSA.
Binciken ya ce kalaman Tinubu game da FCTA da TSA an yi su ne a wajen wannan bikin, ba a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya kamar yadda wasu suka nuna ba.
Masu binciken sun kuma lura cewa wasu ministocin da ke cikin bidiyon sun sauya mukamai tun bayan shekarar 2024.
Haka kuma, Abubakar Momoh ya fito a bidiyon lokacin yana Ministan Raya Yankin Neja Delta, daga baya gwamnati ta soke wannan ma'aikata tare da nada shi Ministan sabuwar Ma'aikatar Raya Yankuna.
Har ila yau, Abdullahi Tijjani Gwarzo, wanda a lokacin yake Ministan Gidaje da Raya Birane, yana cikin bidiyon.
Sai dai an cire shi daga majalisar ministoci a sauyin da Tinubu ya yi a watan Oktoban 2024.
Ko da yake binciken bai iya tabbatar da takamaiman ranar da aka dauki bidiyon ba, alamomin da ke cikinsa sun nuna cewa an dauke shi ne tsakanin shekarar 2023 da 2024.

Kara karanta wannan
'Dan gwamna ya tada ƙura da ya saki bidiyo yana rera wakar sukar Tinubu da mahaifinsa
Saboda haka, binciken ya nuna cewa bidiyon da ke nuna Tinubu da ministoci suna rera tsohuwar wakar kasa ba sabon bidiyo ba ne, kuma ikirarin da ake yadawa a shafukan sada zumunta ba gaskiya ba ne.
Gwamnati ta tilasta koyon taken ma'aikata
A wani labarin, an ji cewa Gwamnatin Tarayya ta dawo da sabon taken ma'aikatan Gwamnatin Tarayya domin kara musu kaimi da kishin kasa.
Shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack ta tabbatar da haka inda ta ce hakan yana da fa'ida Wannan na zuwa ne bayan.
Gwmanatin Tarayya ta sauya taken Najeriya wanda har yanzu wasu ke cigaba da koyo yayin da yan kasa ke korafi.
Asali: Legit.ng
