Ahmad Lawan: Kotu Ta ba da Umarni kan Shari’ar Neman Hana Sanatan Tikiti

Ahmad Lawan: Kotu Ta ba da Umarni kan Shari’ar Neman Hana Sanatan Tikiti

  • Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin yi wa Sanata Ahmad Lawan isar da takardun ƙara ta wata hanya bayan an kasa samun shi
  • Hassan Kafayos ya kalubalanci zaɓen fitar da gwani na APC a Yobe ta Arewa, yana zargin an hana shi takara ba bisa doka ba
  • Kafayos ya roƙi kotu ta soke zaɓen, ta hana INEC amincewa da Lawan, ko ta ayyana shi ɗan takarar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da buƙatar bayar da umarnin isar da takardun ƙara Sanata Ahmad Lawan.

Alƙali Salim Ibrahim ya yanke hukuncin ne bayan lauyan Hassan Kafayos, Francis Mgboh, ya gabatar da ƙorafin ba tare da sanar da ɓangaren da ake ƙara ba.

Kotu ta ba da umarni kan Ahmad Lawan game da zaben fitar da gwani
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan. Hoto: Ahmed Ibrahim Lawan.
Source: Facebook

Dalilin shigar da kara kan Sanata Ahmad Lawan

Kara karanta wannan

Yawan kujerun sanatoci da APC, PDP ke da su a majalisa bayan zaben cike gurbi

Kafayos ya shigar da ƙara yana neman kotu ta soke zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC na mazabar Yobe ta Arewa da aka gudanar ranar 18 ga Mayun 2026, cewar Daily Trust.

Zaben da aka gudanar shi ne ya fitar da Lawan a matsayin ɗan takara, lauyansa ya ce an nemi umarnin ne saboda jami'in kotu ya kasa isar wa Lawan takardun ƙarar kai tsaye.

Lauyan ya kuma zargi Sanata Lawan da kauce wa karɓar takardun ƙarar, saboda haka ya roƙi kotu ta ba da izinin isar da takardun ta hannun duk wani baligi da ke ofishin shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Dattawa, wanda Lawan ke jagoranta.

Bayan amincewa da buƙatar, kotun ta ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 20 ga Yulin 2026.

A zaman da ya gabata, lauyan Kafayos da kuma lauyan APC, Adedayo Adedeji, SAN, ne kaɗai suka halarci kotun.

A cikin ƙarar, Kafayos ya shigar da APC, shugaban jam'iyyar na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, Ahmad Lawan da kuma INEC a matsayin waɗanda ake ƙara. Ya nemi kotu ta ba shi hukunce-hukunce guda huɗu kan rikicin.

Ya ce an hana shi shiga zaɓen fidda gwani duk da kasancewarsa cikakken ɗan APC mai biyan kuɗin rajista, cewar BusinessDay.

Kara karanta wannan

Lamuran siyasa 6 da ka iya tasiri a zaɓen Najeriya na shekarar 2027

Ana artabu kan tikitin takarar sanata Ahmad Lawan
Taswirar jihar Yobe da Sanata Ahmad Lawan ya fito. Hoto: Legit.
Source: Original

Ana zargin APC ta saba dokar kasa

A cewarsa, hakan ya saɓa da sashe na 42 na kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokokin zaɓe na shekarar 2026.

Kafayos ya kuma yi zargin cewa APC ta karya sashe na 84 zuwa na 87 na dokar zaɓe da kuma kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Ya ce matakin ya tauye dimokuraɗiyyar cikin gida da ƙa'idojin gudanar da zaɓen fidda gwani.

Saboda haka ya roƙi kotu ta hana APC da shugaban jam'iyyar miƙa sunan Lawan ga INEC a matsayin ɗan takarar maslaha.

Haka kuma ya nemi a hana INEC karɓa ko wallafa sunan Lawan saboda abin da ya kira zaɓen da ya kasance cike da kura-kurai.

Ya kuma nemi kotu ta umarci APC, shugabanta da INEC su gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani ko kuma su ayyana shi a matsayin halastaccen ɗan takarar jam'iyyar domin zaɓen 2027.

Baya ga haka, Kafayos ya nemi a tilasta APC, Nentawe Yilwatda da Lawan su biya shi diyyar Naira miliyan 50 saboda cire shi daga takarar ba bisa ƙa'ida ba, abin da ya ce ya saɓa wa dokokin zaɓe da kundin tsarin mulkin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Dan a mutun Tinubu ya kare Oluremi, ya ba da labarin attajira mai sayar da ƙosai a Abuja

Sauya suna: Dan talara ya yiwa APC gardama

An ji cewa Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sauya sunayen wasu 'yan takara da suka samu nasara a zaben fitar da gwanin da ta gudanar.

Dan takarar kujerar sanatan Taraba ta Arewa, Hon. Kabiru Bello Badawaire, ya fito ya yi magana kan batun cewa an sauya sunansa da na sanata mai ci.

Kabiru Bello Badawaire ya musanta cewa ya janye daga takarar, inda ya tunatar da APC kan ta bi ka'ida yadda ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.