Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Gaji da Ita, Ya Koma APC a Sokoto

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a PDP Ya Gaji da Ita, Ya Koma APC a Sokoto

  • Ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyyar PDP a Sokoto ya fice daga cikinta zuwa APC mai mulki a jihar
  • Dan siyasar ya danganta matakin da jagorancin Sanata Aliyu Wamakko da ayyukan Gwamna Ahmed Aliyu ke yi
  • An karɓi tsohon ɗan takarar gwamna a gidan Wamakko da ke Abuja, inda APC ta ce sauyin ya nuna jam'iyyar na ƙara samun karɓuwa a Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Tsohon ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen 2023 a Sokoto, ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

Saidu Umar Ubandoma ya ce jagorancin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya jawo hankalinsa komawa cikin jam'iyyar.

Jigon PDP ya koma APC a Sokoto
Tsohon ɗan takarar gwamna a PDP, Saidu Ubandoma da Aliyu Magatakarda Wamakko. Hoto: Sen. Aliyu Magatakarda Wamakko.
Source: Facebook

Mai taimaka wa Wamakko kan yaɗa labarai, Bashar Abubakar, ya bayyana sauyin jam'iyyar cikin wata sanarwa, cewar Tribune.

An karbi jigon PDP a Sokoto

Kara karanta wannan

2027: Maza da mata sun fito gangamin nuna goyon baya ga tazarcen Tinubu a Kwara

Tsohon Kwamishinan Kuɗi kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Sokoto a zamanin Aminu Waziri Tambuwal ya samu karɓuwa daga Sanata Wamakko a gidansa da ke Asokoro, Abuja.

Ya ce wannan ya nuna APC na ƙara samun goyon baya inda Wamakko ya bayyana cewa sauyin Ubandoma ya ƙara wa APC ƙarfi a siyasar Sokoto.

Ubandoma ya ce shugabannin siyasa na ci gaba da amincewa da jagoranci da manufofin jam'iyyar, cewar rahoton Daily Post.

Ya tabbatar wa Ubandoma da magoya bayansa cewa za su samu adalci da cikakken haɗin kai. Ya ce APC gida ce ga masu kishin haɗin kai da ci gaban Sokoto.

Tsohon ɗan takarar PDP da ya dawo APC ya yabawa Wamakko
Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko yana jawabi a taro. Hoto: Sen. Aliyu Magatakarda Wamakko.
Source: UGC

Alkawarin da Wamakko ya yi ga Ubandoma

Wamakko ya ƙara da cewa jam'iyyar za ta bai wa Ubandoma da mabiyansa damar daidai da sauran mambobi, tare da maraba da duk masu son ci gaban al'umma.

Da yake bayani, Ubandoma ya ce salon jagorancin Wamakko da ƙwarewarsa a siyasa sun ba shi kwarin gwiwar shiga APC mai mulki.

Ya kuma yabawa Gwamna Ahmed Aliyu saboda ayyukan raya ƙasa da ya ce sun shafi jama'a kai tsaye a sassa daban-daban na Sokoto.

Kara karanta wannan

Yawan kujerun sanatoci da APC, PDP ke da su a majalisa bayan zaben cike gurbi

Ubandoma ya ce gwamnatin ta samu nasarori a ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, noma da bunƙasa karkara, waɗanda suka ƙarfafa imaninsa da APC.

A cewarsa, waɗannan nasarori sun tabbatar masa cewa APC ce mafi dacewa wajen ci gaba da bunƙasa da wadata a faɗin Sokoto.

Ubandoma ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023, daga baya ya koma ADC kafin ya sake sauya sheƙa zuwa APC.

Ana kallon wannan mataki a matsayin wanda zai iya sake fasalta yanayin siyasar Sokoto, musamman yayin da ake tunkarar zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Wamakko ya karyata shirin maye gurbin Shettima

A baya, an ji cewa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi martani kan batun cewa yana da burin zama mataimakin shugaban ƙasa a 2027.

Tsohon gwamnan Sokoto ya musanta cewa yana da niyyar maye gurbin Kashim Shettima a babban zaɓen 2027 da ake tunkara.

Sanatan ya nuna ya maida hankalinsa ne wajen kawo abubuwan ci gaba ga mutanen da yake wakilta a majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.