'Ni Ma Na fi Karfinsa bare Tinubu': Minista Ya Yi wa Peter Obi Shagube kan Zaɓen 2027
- Ministan Ayyuka, David Umahi, ya yi magana kan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NDC, Mr. Peter Obi
- Umahi ya ce Peter Obi ba barazana ba ne ga Shugaba Bola Tinubu ko APC, yana mai kiran goyon bayan Obi da "siyasar AI"
- Ministan ya soki tarihin mulkin Peter Obi a Anambra, yana zarginsa da kasa gyara hanyoyi, kafa masana'antu, tashar jirgin sama da tashar ruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan ya kare sauye-sauyen gwamnatin Tinubu, yana cewa tattalin arziki na bukatar lokaci kafin ya farfaɗo.
David Umahi, ya yi watsi da tasirin siyasar Peter Obi, yana mai cewa tsohon gwamnan Anambra ba barazana ba ne ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko Jam'iyyar APC.

Source: Twitter
Umahi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da yan jarida inda ya ce ikirarin cewa APC na tsoron Peter Obi ba shi da tushe, cewar PM News.
Umahi ya soki siyasar Peter Obi
Ya bayyana goyon bayan da ake bai wa Peter Obi a matsayin "siyasar AI", yana mai cewa babu wani dalilin da zai sa Tinubu ko APC su ji tsoronsa.
Umahi ya ce shi kansa ba ya tsoron Peter Obi, balle kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko jam'iyyar APC, ya ƙara da cewa Obi ya san ba zai iya fafatawa da shi ba.
Ministan ya kuma soki tarihin mulkin Peter Obi a Anambra, ya tambayi irin nasarorin da ya samu lokacin yana gwamna.
Umahi ya ce ya karanta rahoton da ke cewa Peter Obi ya buƙaci Tinubu ya yi murabus, sai dai ya ce Obi ba shi da hurumin ɗabi'a na yin irin wannan kira.
Ya tambaya sau nawa Peter Obi ya yi murabus saboda gaza gyara hanyoyi, kafa masana'antu, samar da ayyukan yi, gina tashar jirgin sama, tashar ruwa ko biyan 'yan kwangila.

Source: Getty Images
Zargin da Umahi ya yi kan Obidents
Umahi ya kuma zargi ƙungiyar Obidient da rashin haƙurin karɓar ra'ayin da ya saɓa da nasu, cewar rahoton The Sun.
A cewarsa, idan mutum ya saɓa wa Peter Obi, sai a kai shi kotu, ya tambaya sau nawa aka zagi Tinubu ba tare da ya kai mutane kotu ba.
Ya ce irin wannan ɗabi'a na tayar da tambaya kan salon siyasar da ƙungiyar Obidient ke nunawa da kuma irin shugabancin da suke son gabatarwa.
Umahi ya ƙalubalanci mambobin ƙungiyar Obidient da su yi muhawara da shi kan ayyukan gine-gine da sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
Ya ce babu wani ɗan adawa da zai iya yin abin da Tinubu ke yi, musamman wajen sauye-sauyen tattalin arziki da ci gaban ƙasa.
'Kwankwaso zai samu matsala kan Obi' - Sherrif
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya ce Peter Obi ba zai samu goyon bayan mafi yawan masu kada kuri'a daga Arewa ba a zaben 2027.
Ya bayyana cewa duk da an samu hadin kai a tsakanin Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wannan ba zai jawo hankalin Kanawa wajen zaben yan takarar ba.
Ali Modu Sheriff ya kuma bayyana cewa a yanzu haka, mutanen Kano za su juya wa zaben Kwankwaso bayya matukar yana a matsayin mataimakin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng

