Takaitaccen tarihin gwagwarmaya da rayuwar Atiku Abubakar - dan takarar shugaban kasa na PDP a 2019

Takaitaccen tarihin gwagwarmaya da rayuwar Atiku Abubakar - dan takarar shugaban kasa na PDP a 2019

Atiku Abubakar dai dan asalin wani gari ne da ake kira Jada, jihar Adamawa kuma an haife shi ne a ranar 25 ga watan Nuwamba, 1946 kuma shi kadai ne ya rayu a cikin 'ya'yan da mahaifan sa suka haifa a tare.

Da farko dai mahaifin Atiku Abubakar bai bari ya shiga makarantar boko ba saboda irin kyamar da yake yi ma abun har sai da aka tursasa shi kuma iyayen sa sun rabu da junan su tun kafin shi Atikun ya girma ma.

Takaitaccen tarihin gwagwarmaya da rayuwar Atiku Abubakar - dan takarar shugaban kasa na PDP a 2019
Takaitaccen tarihin gwagwarmaya da rayuwar Atiku Abubakar - dan takarar shugaban kasa na PDP a 2019
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya cancanci lambar yabo daga wurin mu - Kwankwaso

Atiku Abubakar yayi karatu a makarantu da dama kafin daga bisani ya soma aiki a hukumar Kwastam ta kasa a shekarar 1969.

Atiku Abubakar ya auri mata 5 a rayuwar sa da suka hada da Titilayo Albert, Ladi Yakubu, Gimbiya Rukayyatu da kuma Fatima Shettima kafin daga bisani ya saki Ladi ya kuma auro Jennifer Iwenjora da ta sauya sunan ta zuwa Jamila.

Atiku Abubakar ya shahara wajen kudi sakamakon kasuwanci da noma da kiwo da ya rika yi a tun a lokacin yana babban jami'I a hukumar Kwastam kafin daga bisani yayi ritaya ya shiga gwagwarmayar siyasa gadan-gadan.

Haka zalika Atiku ya nemi mukaman siyasa a lokuta daban daban inda har ma a shekarar 1998 ya zama gwamnan jihar Adamawa kafin daga bisani Obasanjo ya bashi mukamin mataimakin shugaban kasa.

Tun daga wannan lokacin ne Atiku Abubakar yake ta hankoron ganin ya zama shugaban kasar Najeriya amma har yanzu Allah bai nufa ba.

Yanzu haka dai shine zai jagoranci jam'iyyar PDP a Najeriya a zabukan shekarar 2019 inda ake sa ran zai kara da shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel