Gwamnan Alia Ya Bugi Kirji, Ya Fadawa Tinubu Yawan Kuri'un da Zai Samu a Benue
- Gwamna Hyacinth Alia ya yi alkawarin samar wa Shugaba Bola Tinubu kuri'u akalla 620,000 a Benue yayin babban zaben shekarar 2027 mai zuwa
- Alia ya ce shigar tsohon gwamna Gabriel Suswam jam'iyyar APC zai kara wa jam'iyyar karfi da damar samun gagarumar nasara a jihar a 2027
- Gwamnan ya kuma bayyana cewa ya yi wa shugaban kasa bayani kan tsaro rikicin 'yan gudun hijira da shirye-shiryen noma a jihar Benue
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana cewa zai tabbatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu akalla kuri'u 620,000 a jihar a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Alia ya bayyana hakan ne ranar Litinin bayan ganawarsa da Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock a Abuja, tare da tsohon gwamnan jihar, Sanata Gabriel Suswam.

Kara karanta wannan
Mai martaba Sarkin Ilorin ya yi wa 'yan takarar APC addu'a ta musamman gabanin zaben 2027

Source: Twitter
Gwamna Alia ya ba Tinubu kwarin gwiwa
Ya ce shigar Suswam cikin jam'iyyar APC na daga cikin abubuwan da za su kara wa jam'iyyar karfi a jihar, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.
Gwamna Alia ya ce:
"Ina da cikakken yakinin cewa kamar yadda na lashe zabe a karon farko, za mu ninka yawan kuri'un da shugaban kasa zai samu.
"APC za ta ci gaba da kasancewa jam'iyya mafi karfi, kuma za mu yi abin da zai amfani shugaban kasa da kuma al'ummar Benue baki daya.
A zaben shugaban kasa na 2023, Tinubu ya samu kuri'u 310,468, yayin da Peter Obi ya samu 308,372, inda bambancin kuri'un ya kasance 2,096 kacal.
Aliya ya fadawa Tinubu halin da Benue ke ciki
Sakamakon ya sauya salon siyasar Benue, wadda ta dade tana karkashin jam'iyyar PDP a zamanin tsohon gwamna Samuel Ortom, wanda ya fito fili ya goyi bayan Peter Obi a wancan zabe.
Alia ya ce ya yi amfani da ziyarar wajen yi wa shugaban kasa bayani kan halin tsaro a jihar, matsalar 'yan gudun hijira, kakar noma da kuma yanayin siyasa bayan zaben fidda gwani na APC, in ji rahoton FRCN.
Ya ce hare-haren tsaro da aka rika fuskanta sun ragu, amma har yanzu akwai bukatar a ci gaba da magance damuwar da ke akwai, musamman wajen tabbatar da dawowar 'yan gudun hijira gidajensu cikin aminci.
Gwamna Alia ya yarda akwai sabani a APC
Gwamnan ya kuma ce ya sanar da Tinubu cewa tsohon gwamna Gabriel Suswam ya shiga APC, yana mai cewa mutum mai irin matsayinsa ya dace ya gana kai tsaye da shugaban kasa.
Sai dai Alia ya amince cewa akwai wasu sabani a cikin APC a Benue bayan zaben fidda gwani, amma ya nuna kwarin gwiwar cewa za a shawo kansu.
Asali: Legit.ng
