Abin Tausayi: Ƴaƴan Tsohon Mataimakin Gwamnan Bauchi Sun Rasu a Hatsarin Mota
- Tsohon mataimakin gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela, ya rasa 'ya'yansa biyu dalilin hatsarin mota
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa yaran sun mutu ne a mummunan hatsarin mota a hanyar Bauchi zuwa Azare a jihar
- Gwamna Bala Mohammed ya jajanta wa Baba Tela, ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa mamatan tare da bai wa iyalansu juriyar wannan rashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Tsohon mataimakin gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela, ya rasa 'ya'yansa biyu a wani mummunan hatsarin mota.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar 4 ga watan Yulin 2026 a jihar Bauchi.

Source: Original
Sakon ta'aziyya daga Gwamna Bala
A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan Bauchi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu wanda ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan
2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja
Ya ce yana jajanta wa Sanata Baba Tela bisa rasuwar ƙaunatattun 'ya'yansa, Mustapha da Ummi, da suka mutu a hatsarin mota.
Gwamnan ya bayyana cewa ya karɓi labarin cikin matuƙar kaɗuwa da baƙin ciki, yana mai cewa wannan babban abin takaici ne ga Bauchi.
Ya ƙara da cewa rasuwar matasa biyu cikin irin waɗannan yanayi ta girgiza iyalansu tare da jefa al'ummar Bauchi cikin alhini.
Gwamna Bala Mohammed ya yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba mamatan mafaka a Aljannatul Firdaus da gafarta musu kura-kuransu.
Haka kuma ya roƙi Allah Ya ba iyayensu, 'yan uwansu, abokansu da duk masu alhini haƙuri da juriyar ɗaukar wannan babban rashi.
Ya buƙaci iyalan da suka yi rashin su rungumi ƙaddarar Allah, yana tunatar da su cewa kowace rai za ta koma ga Mahaliccinta.

Source: Facebook
Yadda yaran suka yi hatsarin mota
Mustapha da Ummi sun rasu ne yayin da motar da suke ciki ta yi hatsari a kan hanyar Bauchi zuwa Azare, cewar Tribune.
Lamarin ya faru ne lokacin da suke dawowa Bauchi daga Azare, hedikwatar ƙaramar hukumar Katagum, bayan wata tafiya da suka yi.
Rahotanni sun bayyana cewa su biyun sun rasu nan take sakamakon hatsarin, sannan aka kai gawarwakinsu wani asibiti da ke Bauchi.
A can ne likitoci suka tabbatar da rasuwarsu bayan an gudanar da binciken da ya dace kan halin da suke ciki lamarin da ya tayar da hankalin al'umma.
An tsara gudanar da sallar jana'izar mamatan a ranar Lahadi, 5 ga Yulin, 2026, a fadar Sarkin Bauchi da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
Tsohon Kwamishina a Gombe ya rasu
An ji cewa an yi rashi a jihar Gombe na tsohon kwamishinan da ya yi aiki a gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya tsawon shekaru.
Tsohon kwamishinan yada labarai da al'adu na jihar Gombe, Hon. Ibrahim El-Hassan Kwami, ya yi bankwana da duniya bayan jinyar rashin lafiya.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya aike da sakon ta'aziyyarsa bisa rasuwar marigayin wanda suka taba yin aiki tare a gwamnati.
Asali: Legit.ng
