Hadimin Gwamna kuma Tsohon Kwamishina a Bauchi Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Gwamna Bala Mohammed ya yi alhinin rasuwar hadiminsa kuma tsohon Kwamishinan Harkokin Addini a jihar Bauchi
- Marigayin ya kasance Mai Ba Gwamna Shawara kan Ilimi Mai Zurfi, inda ya ba da gudunmawa wajen bunƙasa ilimi da ci gaban Bauchi
- Gwamnan ya ce Hamza ya kasance mutum mai gaskiya, jajirtaccen bawan jama'a kuma malami, tare da addu'ar Allah Ya gafarta masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana matuƙar alhininsa kan rasuwar dattijo, masani a fannin ilimi kuma tsohon Kwamishinan Harkokin Addini.
Marigayin Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza ya rasu ne a Abuja bayan ya shafe lokaci yana fama da doguwar jinya, lamarin da ya jefa iyalansa da al'ummar Bauchi cikin jimami.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani saƙon ta'aziyya da ya fitar a ta bakin hadiminsa, Mukhtar Gidado wanda ya wallafa a Facebook.
Gwamna Bala ya fadi kyawawan halayen marigayin
Sanarwar ta ce gwamnati da al'ummar Bauchi, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin bawan jama'a nagari mai gaskiya.
Ya ce rayuwar Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza ta kasance cike da riƙon amana, tawali'u, hidima ba tare da son kai ba da jajircewa wajen bunƙasa ilimi.
Kafin rasuwarsa, marigayin ya kasance Mai Ba Gwamna Shawara kan Ilimi Mai Zurfi, inda ya yi amfani da gogewarsa wajen inganta harkokin ilimi.
Gwamna Bala Mohammed ya ce hikima, ƙwarewa da jajircewar marigayin sun taimaka ƙwarai wajen ci gaban fannin ilimi a Bauchi.
Ya ƙara da cewa marigayin ya ba da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa ilimi tun daga tsohuwar Bauchi har zuwa Bauchi ta yanzu.
A cewarsa, irin gudunmawar da ya bayar za ta ci gaba da zama abin koyi ga al'ummomi da kuma masu tasowa nan gaba.

Source: Original
Gwamna ya fadi gudunmawar marigayin a Bauchi
Gwamnan ya kuma tuna irin hidimar da marigayin ya yi a muƙaman gwamnati daban-daban, musamman a matsayin Kwamishinan Harkokin Addini.
Ya ce daga baya marigayin ya ci gaba da hidima a matsayin Mai Ba Gwamna Shawara kan Ilimi Mai Zurfi cikin aminci da ƙwarewa.
Gwamna Bala Mohammed ya ce shawarwari masu amfani da ilimin marigayin sun taimaka wajen tsara manufofi da shirye-shiryen gwamnati masu amfani ga jama'a.
Ya ce:"Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza ya kasance ɗan kishin ƙasa, ƙwararren masani a ilimi, mai renon matasa da kuma mai haɗa kan al'umma."
Ya ƙara da cewa gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi da kyawawan ɗabi'u za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa har abada.
Gwamnan ya bayyana cewa rasuwar marigayin babban rashi ne ga iyalansa, gwamnatin Bauchi, al'ummar jihar baki ɗaya da ma ƙasa gaba ɗaya.
Ya yi addu'ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta wa Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza kura-kuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.
Tsohon mataimakin gwamna ya rasa ƴaƴansa
A wani labarin, an ji cewa tsohon mataimakin gwamnan Bauchi, Sanata Baba Tela, ya rasa 'ya'yansa biyu dalilin hatsarin mota.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa yaran sun mutu ne a mummunan hatsarin mota a hanyar Bauchi zuwa Azare a jihar.
Gwamna Bala Mohammed ya jajanta wa Baba Tela, ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa mamatan tare da bai wa iyalansu juriyar wannan rashi.
Asali: Legit.ng

