Hadimin Abba Ya Nanata Zargin da ake Yi wa Abdusalam Gwarzo na Kwana da N308m

Hadimin Abba Ya Nanata Zargin da ake Yi wa Abdusalam Gwarzo na Kwana da N308m

  • Hadimin gwamnan Kano, Musa Falaki ya fitar da bayanai a kan yadda ake zargin tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo da karkatar da kudin takalawa
  • Sheikh Musa Falaki ya bayyana cewa zargi kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo da karkatar da Naira miliyan 308 da aka ce an ware da sunan addu'o'i
  • Falaki ya ce an tattara Naira miliyan 44 duk wata daga ƙananan hukumomi 44 na tsawon watanni bakwai da sunan ba wa malamai a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Mai ba gwamnan Kano shawara na musamman kan harkokin makarantun Tsangaya, Sheikh Musa Falaki nanata zargin da gwamnati ke yi wa tsohon mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

Ya bayyana hanyar da aka bi wajen karkatar da Naira miliyan 308 da aka ce an tara domin gudanar da addu'o'i na musamman a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Kara karanta wannan

DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya

An zargi hadimin gwamna na wawashe miliyoyin Naira daga asusun kananan hukumomi
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takara a jam'iyyar NDC Hoto: Comr Aminu Abdussalam Gwarzo
Source: Twitter

Ya bayyana haka ne ta cikin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon Hikima wanda suka wallafa a shafin Facebook na kafar.

Zargin da ake yi wa Kwamred Aminu Gwarzo

A cikin hirar, Sheikh Musa Falaki ya ce tsohon shugabancin ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Kano ya sanar da cewa an tara wa Kwamred Aminu Abdussalam kudi.

Ya yi zargin cewa ƙananan hukumomi 44 sun riƙa bayar da gudunmawar Naira miliyan 44 a kowane wata na tsawon watanni bakwai domin shirya addu'o'i na musamman.

An zargi Kwamred Gwarzo da karban Naira miliyan 44 daga kananan hukumomi
Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar NDC Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Comr Aminu Abdussalam Gwarzo
Source: Facebook

Ya bayyana cewa shi da Sheikh Ibrahim Sheshi Maihula ne aka tsara za su jagoranci shirye-shiryen addu'o'in, amma ba su san cewa ana karɓar kuɗi da sunansu ba.

Falaki ya yi zargin cewa shi da Sheikh Ibrahim Sheshi Maihula ba su karɓi ko sisi daga cikin kuɗin ba, kuma ba su gudanar da addu'o'in da aka ce an ware kuɗin dominsu ba.

Kara karanta wannan

Uba Sani: Tinubu ya fi kowane shugaban Najeriya kawo ci gaba a Arewa

Yadda aka binciken Abdussalam Gwarzo

Sheikh Musa Falaki ya ce sun fara jin labarin fitar da kuɗin ne bayan da Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta gayyace su domin amsa tambayoyi yayin gudanar da bincike.

A cewarsa, a lokacin binciken ne suka gano cewa ana zargin an riƙa fitar da Naira miliyan 44 a kowane wata na tsawon watanni bakwai, wanda ya kai jimillar Naira miliyan 308.

Sheikh Falaki ya yi zargin cewa tun da ba su karɓi kuɗin ba, kuma ba a gudanar da addu'o'in da aka ware kuɗin dominsu ba, to Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya karkatar da dukkannin kuɗin da aka ware domin wannan aiki.

Ya ƙara da cewa wannan batu na cikin binciken da PCACC ke yi, inda ya ce an kuma buƙaci Gwarzo ya mayar da sama da Naira miliyan 700 da ake zargin an karkatar daga asusun ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Kara karanta wannan

Uba Sani: 'Yan sanda sun kama mutum 100 kan kisan Ummulkhairi a Kaduna'

Dan Aminu Abdussalam Gwarzo ya kai kara

A baya, mun kawo labarin cewa Mujahid Aminu Abdussalam Gwarzo ya kai ƙarar Sunusi Bature Dawakin Tofa ga kwamishinan 'yan sandan Kano kan zargin ɓata sunan mahaifinsa, wato tsohon mataimakin gwamnan Kano.

Ƙarar ta ce Sunusi Bature Dawakin Tofa ya yi kalaman da suka danganta Aminu Gwarzo da karɓar “Awalaja” daga shugabannin ƙananan hukumomi 44 wanda ake zargin ya yi almundahanarsu ne.

Lauyan mai ƙarar ya buƙaci rundunar 'yan sanda ta binciki lamarin tare da ɗaukar matakin doka kan zarge-zargen da mai magana da yawun gwamnan ya yi tare da daukar matakin da ya dace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng