Kofin Aisha Buhari: Minista ya bada tallafin N50m domin gasar ƙwallon ƙafa

Kofin Aisha Buhari: Minista ya bada tallafin N50m domin gasar ƙwallon ƙafa

  • Sunday Dare, ministan matasa da wasanni na Nigeria ya bada tallafin N50m ga masu shirya gasar cin kofin A'isha Buhari
  • An shirya gasar ne na cin kofin kwallon kafa na mata domin ƙasashen Afirka shida su fafata tsakanin su
  • Kasashen da za su fafata a gasar sun hada da Morocco, Cameroon, Afirka ta Kudu, Cote D'Ivoire, Ghana, Mali da Nigeria

Ministan matasa da cigaban wasanni, Sunday Dare, ya bada tallafin Naira miliyan 50 ga kwamitin shirya gasar cin kofin kwallon ƙafa na A'isha Buhari, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ministan wanda ya sanar da hakan a ranar Talata lokacin da kwamitin ta ziyarce shi a ofishinsa, ya ce gasar kwallon ƙafa na mata na ƙasa da ƙasa da za a yi a Legas zai iya haɓakka kwallon mata a Nigeria.

Kara karanta wannan

Tsohon ministan Afghanistan ya koma sana'ar siyar da abinci a kasar Jamus

Kofin Aisha Buhari: Minista ya bada tallafin N50m domin gasar ƙwallon ƙafa
Kofin Aisha Buhari: Minista ya bada tallafin N50m domin gasar ƙwallon ƙafa. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya jinjina wa kwamitin shirya gasar bisa aikin da suka yi kawo yanzu duk da ƙallubalen da ake fama da shi a kasar a cewar rahoton na Daily Nigerian.

Ya ce:

"Na san kun fara wannan ne da kuɗi ƙalilan amma duba da irin nasarorin da kuka samu ya nuna cewa kunyi jarumta.
"Na karanta abubuwan da kuke yi da abin da kuka yi a lokacin da na tafi wurin gasar Olympic."

Ministan ya yi alkawarin cewa za a bawa masu shirya gasar dukkan goyon baya da gudunmawa da suke bukata domin gasar zai ƙara saka wa mata sha'awar shiga a dama da su a kwallo.

Tunda farko, shugaban kwamitin shirya gasar kuma mataimakiyar shugaban NFF Seyi Akinwunmi ya yi wa ministan godiya bisa goyon bayan da ya basu.

Kara karanta wannan

Hotunan Gidan da Aka Tsinci Gawar Babban Ɗan Sanatan APC a Kaduna

Ya bayyana cewa shida daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa na mata a Afirka za su hallarci gasar.

Wane kasashe za su buga wasan?

Kasashen sun hada da Ghana, Morocco, Cameroon, Afirka ta Kudu, Mali, Cote D'Ivoire da mai masaukin baki wato Nigeria inda za a buga wasannin.

Kamfanin dillancin labarai na Nigeria ya ruwaito cewa za a fara gasar na cin kofin A'isha Buhari ne daga 13 zuwa 21 na watan Satumba a filin wasanni na Agege da Mobolaji Johnson Arena, Onikan a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: