PDP Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 21 a Adamawa duk da Gwamna Ya Koma APC

PDP Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomi 21 a Adamawa duk da Gwamna Ya Koma APC

  • Jam'iyyar PDP ta samu gagarumar nasara a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas
  • Duk da tana adawa, jam’iyyar ta lashe kujerun shugabannin kananan hukumomi 21 baki daya da na kansiloli 226 da ke fadin jihar
  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta Adamawa, (ADSIEC) ta yaba da yanayin zaman lafiya da hadin kan al’ummar jihar yayin gudanar da zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Adamawa, Nigeria - Jam’iyyar PDP ta samu gagarumar nasara a zaben kananan hukumomin jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 21 da kuma kujerun kansiloli 226 da ke fadin jihar.

PDP .
Tutar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Adamawa (ADSIEC), Mohammed Umar, ne ya sanar da sakamakon a hedikwatar hukumar da ke Yola bayan kammala tattara sakamako.

Kara karanta wannan

Yadda aka karbo gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan ya rasu a hannun 'yan Bindiga

PDP ta lashe dukkan zabe a dukkan mazabu

Mohammed Umar ya bayyana cewa an gudanar da zaben a dukkan mazabu 226 na jihar, inda PDP ta yi nasara a duka zabukan shugabannin kananan hukumomi da na kansiloli.

Sai dai shugaban hukumar bai bayyana jimillar kuri’un da aka kada a lokacin zaben ba a kowane mazaba ba.

ADSIEC ta yaba da zaman lafiya a zaben Adamawa

Shugaban ADSIEC ya yaba wa al’ummar jihar Adamawa bisa yadda suka nuna kwanciyar hankali da hadin kai a lokacin gudanar da zaben.

Ya ce goyon baya da hadin kan jama’a sun taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar gudanar da zaben cikin lumana.

Hukumar ADSIEC ta jinjina wa jami’an tsaro

Mohammed Umar ya kuma nuna godiyarsa ga jami’an tsaro, masu sa ido kan zabe da sauran masu ruwa da tsaki saboda gudunmawar da suka bayar wajen tabbatar da zaman lafiya da nasarar gudanar da zaben a fadin jihar.

Tashar TVC News ta ruwaito cewa an sanar da sakamakon zaben ne a gaban jami’an tsaro, wakilan jam’iyyun siyasa, masu sa ido kan zabe da kuma kwamishinonin hukumar ADSIEC

Kara karanta wannan

An kuma dage shari'ar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufai

Fintiri.
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri yana magana a taron Majalisar zartarwa Hoto: @GovernorAUF
Source: Facebook

Babbar nasara ga jam'iyyar PDP

Wannan sakamako ya kara nuna karfin PDP a jihar Adamawa, inda jam’iyyar ta mamaye dukkan kujerun da aka fafata a wannan zaben kananan hukumomi.

Sai dai nasarar PDP a zaben kananan hukumomin Adamawa na iya zama barazana ga APC duba da yadda gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri ya koma jam'iyya mai mulki a watannin baya.

Gwamnan Adamawa ya gargadi hadimansa

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya gargadi dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa da ba sa goyon bayan jam'iyyar APC.

Gwamna Fintiri ya umarci masu riƙe da muƙaman siyasa da suka ƙi komawa jam’iyyar APC da su yi murabus ko kuma a kore su daga aiki.

Ana ganin matakin gwamnan ba ya rasa nasaba da ƙin bin sa da yawancin masu riƙe da muƙaman siyasar suka yi wajen komawa APC, inda suka ci gaba da kasancewa a jam’iyyar adawa ta PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262