Gwamna Abba Ya Yi Sabon Nadi a Hukuma sakamakon Karin Kwamishinoni a Kano

Gwamna Abba Ya Yi Sabon Nadi a Hukuma sakamakon Karin Kwamishinoni a Kano

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Dr. Suraj Sulaiman a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano
  • Sabon nadin ya biyo bayan kammala wa’adin Dr. Aliyu Isa Aliyu, wanda yanzu haka ya zama Kwamishinan Raya Kiwo
  • Gwamnan ya yaba da kwarewar Dr. Suraj, yana mai cewa zai taimaka wajen inganta tsarin gwamnati ta fuskar dogaro da sahihan bayanai

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Dr. Suraj Sulaiman a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta jihar.

Sanarwar hakan ta fito ne a wata takarda da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi.

Abba ya nada Dr. Suraj mukami a Kano
Hoton Dr. Suraj, Gwamna Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A sakon da ya Sanusi Dawakin Rofa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce nadin ya fara aiki nan take, bayan kammala wa’adin mai rike da mukamin a baya.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya biya iyalin ɗan kwangilan da ya rasu N184m da gwamnatin Ganduje ta hana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliyu Isa Aliyu, da ke dab da zama Farfesa ne tsohon Shugaban hukumar, kuma yanzu haka an nada a matsayin Kwamishinan Raya Kiwo a Kano.

Gwamnan Kano ya ba da sabon umarni

Gwamnatin Kano ta umarci a gudanar da bikin mika mukami tsakanin Litinin da Juma’a na wannan mako domin bai wa sabon shugaban damar kama aiki.

Dr. Suraj Sulaiman kwararre ne a fannin lissafi da bincike, kuma ya shafe shekaru yana koyarwa da gudanar da nazari a bangaren kididdiga.

Ya karɓi digirin digirgir (PhD) a fannin Lissafi daga Universiti Teknologi Malaysia (UTM) tsakanin 2015 zuwa 2018.

Haka kuma yana da digiri na biyu daga jami’ar Yasar, Izmir, Turkiyya (2012–2014), da kuma digiri na farko daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano, Wudil (2006–2010).

Gwamnan Kano ya yabi Dr. Suraj

Sabon Shugaban hukumar kididdiga na Kano tsohon dalibi ne a makarantar share fagen shiga jam'ia ta Kano (CAS), inda ya inda ya karɓi Difloma a fannin koyar da Lissafi (2004–2006).

Kara karanta wannan

Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba da kwarewar Dr. Suraj, yana mai jan hankalin mahimmancin bayanan kididdiga

A sakonsa na taya murna, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa sabon shugaban bisa wannan muhimmin matsayi da aka dora masa.

Abba Kabir Yusuf ya yabi Dr. Suraj
Hoton gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Ya ce yana da yakinin cewa gogewa da kwarewar Dr. Suraj zai taimaka wajen inganta ayyukan hukumar da samar da bayanai.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na da cikakken kuduri wajen kafa tsarin mulki mai dogaro da ingantattun bayanan kididdiga.

A cewar Injiniya Abba Kabir Yusuf, hakan na da matukar muhimmanci wajen tsara shirye-shirye da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a jihar Kano.

Gwamnan Kano ya biya hakkin 'dan kwangila

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da biyan kuɗin kwangila da ya kai Naira miliyan 184.5 ga iyalan marigayi Alhaji Sulaiman Abubakar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin shi ne mai kamfanin Dutsen-Ma, wanda ya samu kwangila daga Ma’aikatar Lafiya a zamanin tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya fusata, ya ajiye mukami bayan sauya shekar Eno zuwa APC a Akwa Ibom

Aikin da aka ba kamfanin ya haɗa da sabunta cibiyar lafiya ta Garo, da ke ƙaramar hukumar Kabo, wanda aka kammala cikin nasara tare da mika takardun da suka dace tun a 2018.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng