2027: Tsohon na Kusa da Peter Obi, Ya Fadi Abin da Tinubu Zai Yi idan Babu Hadaka
- Kenneth Okonkwo ya taɓo batun yunƙurin da ƴan adawa suke yi na kafa haɗaka domin tunkarar Mao girma Bola Ahmed Tinubu a 2027
- Tsohon jigon na jam'iyyar LP ya bayyana cewa cikin sauƙi Tinubu zai koma kan kujerarsa idan ƴan adawa suka kasa dunƙulewa waje ɗaya
- Ya nuna cewa da yawa daga cikin ƴan siyasan da suke komawa APC, suna yin hakan ne bisa tunanin za a rubuta musu sakamakon zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun bakin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP, Kenneth Okonkwo, ya yi magana kan haɗakar ƴan adawa.
Kenneth Okonkwo ya bayyana cewa kafa haɗakar jam’iyyun adawa ita ce kaɗai damar da suke da ita don kayar da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Kenneth Okonkwo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Channels Tv a shirinsu na 'Sunday Politics'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mecece makomar Tinubu idan babu haɗaka?
Tsohon na kusa da Peter Obi ya nuna ƙwarin gwiwa cewa za a kafa haɗakar, duk da bai tabbatar da wanda zai jagorance ta ba.
"Yayin da muka tunkari 2027, na san za a samu haɗakar jam’iyyu. Ko za ta kasance tsakanin Peter Obi da Atiku, ban sani ba, amma tabbas za a kafa haɗaka."
"Me ya sa? Domin wannan ce kaɗai damar da ƴan adawa ke da ita domin su yi tasiri.”
- Kenneth Okonkwo
Da aka sake tambayarsa ko rashin kafa haɗakar zai sa a kasa kayar da Tinubu, Okonkwo ya amsa da cewa zai ci zaɓe ne cikin sauƙi idan ƴan adawa ba su dunƙule waje ɗaya ba.
Ya ƙara da cewa babu ɗan takara guda ɗaya da zai iya kayar da Tinubu a 2027 domin a Najeriya, mun shiga cikin matsalar da ba kawai lashe zaɓe ba ne, dole ne ka tabbatar da nasararka.
Okonkwo ya ƙara da cewa idan manya za su haɗu kamar yadda suka yi a 2014 suka fuskanci Goodluck Jonathan a 2015, za su iya sauke Tinubu daga mulki a 2027.

Asali: Facebook
Dalilin ƴan adawa na sauya sheƙa
Game da sauya sheƙar da wasu ƴan jam’iyyun adawa suke yi zuwa APC, Okonkwo ya ce dalilin hakan shi ne wasu ƴan siyasa na tunanin APC za ta rubuta musu sakamakon zaɓe a 2027.
Ya ce abin mamaki ne yadda mutane ke ganin wurin da ke ƙokarin rugujewa amma suna rugawa cikinsa neman mafaka.
Yayin da ya jaddada murabus ɗinsa daga jam’iyyar LP, Okonkwo ya bayyana cewa bai koma wata sabuwar jam’iyya ba tukuna.
Fasto ya faɗi magajin Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa malamin addini kuma shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele, ya yi hasashen wanda zai gaji Shugaba Bola.Tinubu.
Primate Ayodele ya bayyana cewa mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne zai gaji Tinubu a 2031.
Ya yi kira ga ƴan Najeriya da ka da su bari ƴan siyasa masu yunƙurin kafa haɗaka su yaudare su a zaɓen 2027.
Asali: Legit.ng