Gwamnan Delta Ya Fadi Babban Jigon PDP da zai Koma Jam'iyyar APC

Gwamnan Delta Ya Fadi Babban Jigon PDP da zai Koma Jam'iyyar APC

  • Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi magana kan dandalin siyasar da tsohon gwamnan jihar James Ibori ya samar
  • Sheriff Oborevwori ya bayyana cewa a yanzu wannan dandalin da Ibori ya samar ya tarwatse kuma kowa ya kama gabansa
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa yana sa ran nan ba da jimawa ba James Ibori zai haɗe da su a jam'iyyar APC mai ci
  • Mai girma Gwamna Oborevwori na zuwa ne bayan shi da kusan daukacin jiga-jigan PDP a jihar Delta sun sauya sheƙa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya ce yana sa ran tarbar tsohon gwamnan jihar, James Ibori, cikin jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba.

A ranar 23 ga Afrilu, Gwamna Sheriff Oborevwori tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP a jihar Delta, sun sauya sheƙa zuwa APC.

Gwamna Sheriff Oborevwori da James Ibori
Oborevwori ya yi magana da James Ibori kan komawa APC Hoto: James Ibori, Rt. Hon. Sheriff Oborevwori
Asali: Facebook

The Cable ta ce Gwamna Oborevwori ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron tunawa da Amos Utuama, tsohon mataimakin gwamnan Delta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi taron ne a cocin Katolika na St. Andrew’s da ke Otu-Jeremi, a ƙaramar hukumar Ughelli ta Kudu.

Gwamna Oborevwori na son Ibori ya koma APC

Yayin da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Oborevwori ya jaddada buƙatar haɗin kan siyasa a cikin jihar, yana mai cewa dandalin siyasar da James Ibori ya kafa ya tarwatse.

Ya bayyana cewa ya tambayi Ibori kai tsaye kan lokacin da zai shiga jam'iyyar APC, inda ya nuna kyakkyawan fata cewa tsohon gwamnan zai sauya sheƙa nan kusa, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

“Gaskiya kawai za mu faɗa. Idan kana da son rai, ahalinka zai tarwatse, komai zai lalace."
“Ban so na yi magana a nan ba, amma limaminmu ya ce, ‘yi magana domin mutane su ji’. Kun san cewa dole ne a tuntuɓi dattawa, a nemi shawara daga masu hankali."

"Yayin da ka ke jagorantar ƴaƴanka, wasu na cikin APC, wasu na cikin LP, wasu suna nan, sai na tambaye shi (Ibori), ‘yaushe zai haɗe da mu?’ Kuma na san zai haɗe da mu nan kusa cikin APC. Zan tarbi shugabanmu da sunan Ubangiji.”
"Ka kafa babban gida, kuma wannan gida yana buƙatar haɗin kai."

- Gwamna Sheriff Oborevwori

Gwamna Sheriff Oborevwori
Gwamna Oborevwori ya bukaci hadin kai a siyasar Delta Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Twitter

A watan Disamba na shekarar 2024, Erhiatake Ibori-Suenu, ƴar tsohon gwamna James Ibori kuma mamba a majalisar wakilan Najeriya, ta sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Kuskuren Atiku Abubakar a rikicin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata mai wakiltar Benue ta Kudu, Abba Moro, ya nuna kuskuren Alhaji Atiku Abubakar kan rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP.

Sanata Abba Moro ya bayyana cewa ya kamata Atiku ya ɗauki matsayin jagora domin haɗa kan ƴaƴan PDP bayan rashin nasarar da jam'iyyar ta yi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Ya nuna cewa Atiku ya gaza wajen shawo kan rikicin PDP duk da burin da yake da shi na sake tsayawa takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng