Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da Sanata Ovie Omo-Agege
Ana zargin Sanata Ovie Omo-Agege da daukar hayyar yan daba wanda suka sace sandar majalisar dattawa wanda aka sace ta a yau Labara yayin da ake zaman majalisa amma daga baya aka dawo da ita.
Idan ba'a manta ba, Majalisar da dakatar da Sanata Omo-Agege na kwanaki 91 saboda kalaman daya fada na rashin goyon bayan canja jadawalin zaben 2019 da majalisar tayi kokarin yi a baya.
Tuni dai Yan sanda sunyi kama Sanatan kuma sun tafi dashi a motarsu misalin karfe 1.50 na rana.
Saboda la'akari da abubuwan da ke faruwa game da Sanata yasa Legit.ng ta binciko muku wasu muhimman abubuwa 10 daya kamata ku sani game da Sanatan.
1) Ovie Omo-Agege dai lauya ne
2) Ya kammala kartun digirinsa na farko (LLB) a Jami'ar Benin a 1985, sannan daga bisani ya tafi yayi digiri na biyu (Msc) a Jami'ar Shari'ah na Tulane a 2002.
3) Sanatan dan asalin jihar Delta, yana wakiltan yankin Delta ta tsakiya ne a majlisar dattawa na Najeriya.
DUBA WANNAN: Majalisar Dattijai tayi wurgi da kudirin gyaran jadawalin zaben 2019
4) Sanata Omo-Agege mamba ne na kwamitin Shari'an, kwamitin kare hakkin bil-adama da harkokin shari'ah, Kwamitin man fetur, Kwamitin sufuri da kuma kwamitin sufurin ruwa da muhalli duk a majalisar na dattawa.
5) Shekarun Sanatan 54 a duniya.
6) Sanatan ya lashe zabe ne a karkashin jam'iyyar Labour amma daga baya ya canja sheka zuwa jam'iyyar APC.
7) Yayi aiki a matsayin sakataren gwamnatin jihar Delta a shekarar 2007
8) Ya kuma yi aiki a matsayin kwamishina na ayyuka na musamman a jihar delta daga 2005-207.
9) Ya kuma yi aiki a matsayin mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Delta daga 2003 zuwa 2007.
10) An dakatar da Omo-Agege ne ranar Alhamis da ta gabata saboda kalaman daya fada akan kudirin canja jadawalin zabe da kuma shigar da majalisar kara kotu bayan ya nemi afuwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng