"Barci kawai Yake Yi": An Yi Wa Sanatan APC Barazanar Kiranye daga Majalisa
- Kujerar sanatan Delta ta Tsakiya na shirin fsrs tangal-tangal yayin da yake fuskantar barazanar kiranye daga majalisar dattawan Najeriya
- Wata ƙungiya ta yi buƙaci Sanata Ede Dafinone da ya yi murabus daga kujerarsa ko kuma su yi masa kiranye
- Ƙungiyar ta zargi sanatan da rashin iya wakilci da kuma gazawa wajen gudanar da ayyukan kirki a mazaɓarsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - Wasu daga cikin mazauna mazaɓar sanatan da ke wakiltar Delta ta Tsakiya, Ede Dafinone, sun yi barazanar yi masa kiranye daga majalisar dattawa.
An zaɓi Sanata Ede Dafinone ne a ƙarkashin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023.

Asali: Facebook
Shugaban ƙungiyar Nigeria Polling Unit Forum, wacce ke jagorantar shirin kiranyen, Nicholar Evwienure, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a Asaba a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ake son yi wa Sanata Dafinone kiranye?
Ƙungiyar Nigeria Polling Unit Forum reshen jihar Delta, na zargin Sanata Dafinone da gazawa wajen wakilci da rashin aiwatar da wasu ayyuka.
Nicholas Evwienure ya ce suna kuma neman Sanata Dafinone da ya yi murabus cikin girmamawa.
“Mu masu kaɗa ƙurri’a da aka yi wa rajista a mazaɓar Delta ta Tsakiya, daga jam'iyyu daban-daban, muna kira ga Sanata Ede Dafinone da ya ayi murabus cikin girmamawa, ko kuma mu fara shirin yi masa kiranye daga kujerarsa."
- Nicholas Evwienure
Abel John-Gold, ɗaya daga cikin mazauna yankin, ya nuna cikakken goyon baya ga wannan shirin na yi wa sanatan kiranye daga majalisa.
"Sanata Ede barci kawai yake yi a majalisar dattawa. Ede ya ci amanarmu. Ina goyon bayan a yi wa Sanata Ede Dafinone kiranye."
“Ya gaza a kowane fanni. Ya manta da waɗanda suka yi aiki domin nasararsa. Ya manta da waɗanda suka yi masa kamfen. Ya manta da duk masu goyon bayansa.”
- Abel John-Gold
An buƙaci a yi masa uzuri
Sai dai wani ɗan yankin, Nelson Egware, ya ce har yanzu lokaci bai yi ba da za a yanke hukunci kan ayyukan Sanatan.
“A ganina, bai gaza taɓuka komai ba, domin ba za ka iya auna nasarar ɗan majalisa cikin shekaru biyu kacal ba."
- Nelson Egware

Asali: Facebook
Josephine Omo-Dion, wata mazauniyar yankin, ta kuma roki jama’a da su yi haƙuri su ba shi dama.
Amma a nasa ɓangaren, Adelabu Bodjor, shugaban ma’aikatan ofishin Sanata Ede Dafinone, ya yi watsi da yunƙurin a matsayin wani abu wanda ba zai yi tasiri ba.
Sanata Moro ya fallasa masu komawa APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ya yi wa sanatoci masu komawa APC tonon silili.
Sanata Abba Moro ya bayyana cewa sanatocin da ke rububin komawa jam'iyyar APC mai mulki, masu laifi ne da ke neman samun mafaka.
Abba Moro wanda ke wakiltar Benue ta Kudu ya bayyana cewa galibin masu sauya sheƙar suna yi ne domin su samu gafara ta siyasa.
Asali: Legit.ng