Ana Tsaka da Rigimar Ganduje, Babban Ɗansa Ya Ba da Mamaki a Ofishin Yaki da Cin Hanci

Ana Tsaka da Rigimar Ganduje, Babban Ɗansa Ya Ba da Mamaki a Ofishin Yaki da Cin Hanci

  • Yayin da ake ci gaba da maganganu kan binciken Abdullahi Ganduje, babban dansa ya kai ziyara ofishin hukumar cin hanci
  • Abdulaziz Ganduje ya kai ziyarar ce domin nuna goyon baya kan binciken shugaban jam’iyyar APC da ake yi a jihar
  • Wannan na zuwa yayin da gwamnatin jihar ke tuhumar tsohon gwamnan da matarsa da kuma ɗansa kan badakalar kudi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Babban ɗan shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyara ofishin yaki da cin hanci na jihar Kano.

Abdul’aziz Ganduje ya kai ziyarar ce wurin shugaban hukumar, Magaji Rimingado domin nuna goyon bayansa kan binciken Ganduje da ake yi.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Daga karshe an bayyana wadanda suka 'kitsa' shirin

Abdul'ziz Ganduje ya yabawa hukumar yaƙi da cin hanci a Kano
Babban ɗan shugaban APC, Abdul'aziz Ganduje ya kai ziyara ofishin yaƙi da cin hanci a Kano. Hoto: Muhyi Rimingado, Abdul'aziz Ganduje.
Asali: Facebook

Yaushe ɗan Ganduje ya kai ziyarar?

Abdul’aziz ya kai ziyarar ce a jiya Laraba 17 ga watan Afrilu inda ya ce binciken ya yi dai-dai kuma ya zo a kan gaba, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana goyon bayansa kan tuhumar mahafinsa da mahaifyarsa da kuma ɗan uwansa da hukumar ke yi, a cewar Daily Nigerian.

Wane korafi ɗan Ganduje ya yi?

Sai dai ya nuna damuwa kan yadda aka cire shi a matsayin daraktan wani kamfani da ake bincike ba tare da saninsa ba.

Ya bayyana cewa cire shi da aka yi ba bisa ka’ida ba rashin adalci ne karara wanda ya ce hakan ya sabawa doka.

Abdulaziz Ganduje ya ce wani mai harkar gine-gine ya yi masa magana wurin taimaka masa siyan filaye a Kano inda ya yi masa tayin makudan daloli.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Jam'iyyar APC ta mayar da martani kan hukuncin babbar kotun Kano

Ya ce a cikin tayin har da da kuma kamisho na makudan kudi har N35m domin taimaka masa a siyan filayen a jihar Kano.

Ilyasu Kwankwaso ya magantu kan binciken Ganduje

A baya, kun ji cewa jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya magantu kan binciken tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Kwankwaso ya ce wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka ba a shirye ta ke ba ganin yadda ake gudanar da lamarin a jihar.

Ya kuma zargi Sanata Rabiu Kwankwaso da neman kawo rikici a jam’iyyar domin samun damar shiga APC cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel