Da duminsa: 'Dan gwamnan Kano AbdulAziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Goggo wajen EFCC
- Rashin jituwa ya auku a gidan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
- Dan gwamna, AbdulAziz ya shigar da mahaifiyarsa wajen hukumar EFCC
- Yana zargin uwargidar gwamnan kuma mahaifiyarsa da laifin cin amana
Kano - Hafsat Ganduje, Uwargidar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ta ki amsa gayyatar hukumar EFCC kan karar zargin cin rashawa da 'danta, AbdulAziz Ganduje, ya kai kanta.
Premium Times ta ruwaito cewa an gayyaci Hafsat Ganduje ranar Alhamis da ta gabata hedkwatar EFCC dake Abuja.
Abdulazeez ya kai mahaifiyarsa, Hafsat Ganduje, kara wajen EFCC ne kan zarginta da amfani da karfin mulki wajen tarawa kanta dukiya.
A cewar majiyoyi da suka ga takardar karar da Abdulazeez ya shigar, ya bayyana cewa wani mai gine-gine ya tuntubeshi don samun wasu filaye a Kano da dubban daloli da kuma N35m matsayin la'ada.
Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi
Premium Times ta ce ta samu labarin cewa Abdulaziz yace ya baiwa mahaifiyarsa kudin.
Majiyar tace:
"Bayan watanni uku, mutumin ya gano cewa filayen da yace a samar masa tuni an baiwa wasu mutane daban kuma ya bukaci a mayar masa da kudinsa."
Yayinda aka tuntubi mai magana da yawun gwamnatin jihar Kano, Mohammed Garba, ya bayyana cewa ba zai iya magana kan lamarin ba.
Asali: Legit.ng