Bola Tinubu na Amfani da Kudin da Ya Ci Bashi wajen Gina Ababen More Rayuwa a Najeriya

Bola Tinubu na Amfani da Kudin da Ya Ci Bashi wajen Gina Ababen More Rayuwa a Najeriya

  • Ministan ayyuka, David Umahi ya kare yawan ciyo bashin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke yi tun bayan hawansa mulki
  • Umahi ya ce Tinubu na karbo aron kudi ne domin gina ababen more rayuwa kamar tituna, wanda za a dade ana amfana da su
  • Ministan ya kafa hujja da manyan titunan da gwamnatin Tinubu ke ginawa a sassan kasar nan, ciki har da yankinsa Kudu maso Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa jimillar ayyukan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke gudanarwa, ciki har da wadanda ya gada da sababbi, sun kai darajar Naira tiriliyan 34.

Umahi ya ce wasu ‘yan Najeriya na tambayar dalilin da yasa gwamnati ke ciwo bashi, yana mai cewa ana yin hakan ne domin gina manyan hanyoyi da gadoji masu dorewa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji abin da Tinubu ya shirya yi a shekaru 2 na farko bayan ya ci zaben 2027

Ministan ayyuka.
Ministan ayyuka, David Umahi yayin da ya fita rangadin duba aikin gina tituna a Najeriya Hoto: David Umahi
Source: Facebook

David Umahi ya kare karbar bashi

Jaridar Vanguard ta ruwaito vewa Ministan ya bayyana haka ne yayin duba aikin gina titin Abakaliki zuwa Afikpo a jihar Ebonyi da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

“Abu mai kyau shi ne idan muka ciwo bashi muna zuba su ne a ayyukan more rayuwa, muna sake gina tituna da za a yi tsawon shekaru 100 ana amfani da su,
“Saboda haka idan mutane suka tambayi dalilin ciwo bashi, ku gaya musu cewa muna yin hakan ne domin gina ababen more rayuwa.”

- David Umahi.

Ya ce irin aikin da ake yi yanzu a titunan Najeriya tamkar gina gada ne, saboda za su dawwama na dogon lokaci ba tare da bukatar gyare-gyare ba.

Manyan titunan da Tinubu ke ginawa

Umahi ya bayyana cewa aikin titin Calabar zuwa Ndibe Beach na daya daga cikin manyan ayyukan gadon tarihi na gwamnatin Tinubu, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

An ware Naira Biliyan 1.4 domin saya wa Gwamna Ahmed Aliyu sababbin motocin aiki

A cewarsa, aikin zai kasance hanya mai layi biyu tare da simintin kankare da fitilu masu amfani da hasken rana a tsawon kilomita 123, kuma zai lakume Naira biliyan 454.

Ministan ya kara da cewa ana ci gaba da aiki a bangaren farko na titin da ya taso daga Calabar zuwa Benue, Kogi, Nasarawa har zuwa Apo a Abuja, wanda tsawonsa ya kai kilomita 465.

Ya ce bangare na biyu na titin mai tsawon kilomita 178 wanda zai lakume Naira biliyan 685, yana gudana daga jihar Benue ya bi ta Kogi da Nasarawa zuwa gadar Owete.

Umahi.
Ministan ayyuka, David Umahi tare da Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Umahi ya jaddada goyon bayan Tinubu

Umahi ya ce yankin Kudu maso Gabas ya samu kulawa sosai a gwamnatin Tinubu, yana mai kira ga mutanen yankin da su mara wa shugaban kasa baya.

“Ya kamata mutanen Kudu maso Gabas su yi siyasa cikin hikima ba tare da son zuciya ba. Za mu goyi bayan Shugaba Tinubu kuma ba za mu yi kuskure ba,”

- in ji shi.

Tinubu ya fara shirin wa'adi na 2

A baya, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara bayanin ayyukan da zai yi idan yan Najeriya sun sake zaben shi a karo na biyu a 2027.

Kara karanta wannan

Malami ya yi abin kunya, kotu ta kama shi da laifin dirka wa 'yan mata ciki a Kwara

Da yake amsa tambaya kan abin da ‘yan Najeriya za su iya tsammani a shekaru biyun farko na wa’adi na biyu, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta kara kaimi kan manufofinta.

Ya ce gwamnatinsa ba za ta sassauta ba duk da wahalhalun da ake sha sakamakon tsare-tsaren tattalin arziki, saboda za a ga amfaninsu a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262