Tinubu Ya Kafa Tarihi, Ya Kirkiri Sabon Ofishi a Fadar Shugaban Kasa kan Tsaro
- Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa (Mai Ritaya) domin ƙarfafa tsaron cikin gida da haɗin kan hukumomin leken asiri
- Janar Famadewa ya yi aiki na shekaru sama da 30, inda ya taka rawar gani wajen kafa cibiyar tattara bayanan sirri (IFC) a ofishin NSA
- Babban aikin da ke gaban sabon mashawarcin shi ne samar da dabarun tunkarar barazanar tsaro ta hanyar amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Manjo Janar Adeyinka A. Famadewa (Mai Ritaya) a matsayin Mashawarci na Musamman kan tsaron cikin gida.
Wannan naɗi, wanda ke ƙunshe a cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanya wa hannu, ya nuna aniyar gwamnatin Tinubu na inganta dabarun kare rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan
Jonathan ya amsa kiran 'yan Najeriya, zai tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP

Source: Twitter
Tinubu ya nada mai ba shi shawara kan tsaro
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya fitar da sanarwar nadin sabon mai ba shugaban shawara kan tsaron gida a shafinsa na X a ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.
A cikin sanarwar, George Akume ya ce Janar Famadewa ya kasance tsohon babban jami'in soja ne da ya shafe shekaru sama da 30 yana aiki a fannin tsaro da leken asiri.
"Ya shahara wajen sanin dabarun yaƙi da ta'addanci da kuma diflomasiyyar tsaro a matakin ƙasa da ƙasa," a cewar Akume.
Sanarwar ta ce wannan gogewa tasa ce ta sanya Shugaba Tinubu nuna kwarin gwiwar cewa zai iya bayar da gagarumar gudunmawa ga shirin "Renewed Hope" na shawo kan tsaron Najeriya.
Tarihin ayyukan sabon hadimin Tinubu
A tsakanin shekarar 2015 zuwa 2021, Janar Famadewa ya riƙe matsayin babban jami'in ma'aikata a ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), in ji sanarwar Akume.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
"A wannan lokacin ne ya jagoranci kafa cibiyar fikira ta IFC, wadda ta haɗa kan hukumomin DIA, NIA, DSS, 'yan sanda, da sauran rassan rundunar soji domin samar da sahihan bayanan sirri na bai-ɗaya.
"Bayan ya yi ritaya, bai zauna haka ba, domin ya ci gaba da bayar da gudunmawa a matsayin babban jami'in bincike a cibiyar Nigerian Army Resource Centre da ke Abuja."

Source: Twitter
Manufar nadin sabon hadimin Tinubu
Shugaba Tinubu ya buƙaci Janar Famadewa da ya yi amfani da dukkan kwarewarsa da kishin ƙasa wajen ganin an cimma muradun tsaron Najeriya.
Manufar wannan naɗi ita ce tabbatar da cewa hukumomin tsaro sun haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen gano barazana tun kafin ta auku ta hanyar amfani da fasahar zamani da leken asiri.
Wannan mataki dai na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubale daban-daban na tsaro.
Karanta sanarwar a kasa:
Tinubu ya nada sabon shugaban DSS

Kara karanta wannan
An shiga tashin hankali a Filato, ƴan bindiga sun kashe gomman mutane a sabon hari
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
Fadar shugaban kasa, ta bayyana cewa Ajayi ya maye gurbin Yusuf Magaji Bichi wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a 2018.
Sabon Darakta-Janar na DSS, Mista Adeola Ajayi, ya taka matakai masu yawa kafin ya kai kai matsayin mataimakin darakta janar na hukumar.
Asali: Legit.ng
