ADC Ta Dura Kan Peter Obi, Ta 'Gano' Manufarsa game da Siyasar Najeriya

ADC Ta Dura Kan Peter Obi, Ta 'Gano' Manufarsa game da Siyasar Najeriya

  • Jam'iyyar ADC ta caccaki tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Peter Obi, ta zarge shi da wata manufa
  • Kakakin ADC, Malam Bolaji Abdullahi, ya zargi tsohon gwamnan da rashin sanin manufofin jam’iyyar kafin ficewarsa zuwa NDC
  • Bolaji ya ce Obi ya fi mayar da hankali kan samun tikitin takara maimakon fahimtar tsarin manufofi da akidar jam’iyyar ADC

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya soki tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi a Najeriya.

Bolaji Abdullahi ya soki Obi ne kan zargin rashin sha’awar sanin manufofin jam’iyyar inda ya ce bukatun kansa ne kawai a gabansa.

ADC ta tona wa Peter Obi asiri
Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdulahi yayin ganawa da manema labarai. Hoto: Bolaji Abdullahi.
Source: Facebook

Kakakin jam'iyyar ya bayyana haka ne yayin hira da gidan jaridar Arise TV da aka wallafa a YouTube inda ya bayyana cewa Obi bai da burin ceto kasar.

Kara karanta wannan

Datti Baba Ahmed ya hango matsala tun yanzu a tafiyar Kwankwaso da Peter Obi

Zaben 2027: ADC ta dura kan Peter Obi

Malam Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa Obi bai fahimci matsayar ADC a batutuwa kamar tallafin mai da matsalar tsaro ba.

Ya ce jam’iyyar ta ɗauki watanni tana tsara kundin manufofi domin bayyana yadda za ta tafiyar da mulki idan ta samu dama.

A cewarsa, duk wanda ke son canza Najeriya ta hanyar siyasa ya kamata ya san abin da jam’iyyarsa ta tsaya a kai domin samun sauki game da cin zabe.

Bolaji Abdullahi ya kuma yi zargin cewa wasu ’yan siyasa sun fi sha’awar samun tikitin takara maimakon bin akidar jam’iyya da tsarin dimokuraɗiyya.

Ya bayyana ADC a matsayin jam’iyya mai tsayayyen tsari da manufofi, amma wasu na son amfani da ita kawai wajen cimma burinsu na siyasa.

Kakakin jam’iyyar ya ce duk matsin lambar da gwamnati ta saka wa ADC, jam’iyyar ta ci gaba da jajircewa wajen kare dimokuraɗiyya da muradun jama’a.

ADC ta fadi shirin Peter Obi a Najeriya
Tsohon gwamna, Peter Obi da kakakin ADC, Bolaji Abdulahi. Hoto: Mr Peter Obi, Bolaji Abdullahi.
Source: Facebook

'Abin da Obi ya taba fada' - ADC

Kara karanta wannan

ADC: Gaskiyar Abin da ya kori Obi da Kwankwaso zuwa NDC

Bolaji Abdullahi ya tuna cewa a baya Obi ya taɓa faɗin cewa idan ’yan adawa suka tsaya da ’yan takara biyu, hakan zai bai wa Bola Ahmed Tinubu nasara a 2027.

Ya ƙara da cewa Peter Obi ya samu gata sosai a ADC har aka ba shi damar zaɓar wanda zai riƙe muhimmin ofishin sakataren shirye-shirye na jam’iyyar.

Bolaji ya ce ficewar Obi da Rabiu Musa Kwankwaso zuwa NDC ba sabon abu ba ne, domin an fara shirinta tun bayan wata ganawa da suka yi a Kano.

ADC ta magantu kan fitar da dan takara

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar ADC ta bayyana cewa za ta zaɓi ɗan takarar shugaban kasa ta hanyar amfani da tsarin maslaha domin zaben badi.

Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana wannan shirin ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Litinin, 4 ga watan Mayun 2027.

Bayanan na Bolaji Abdullahi sun fito ne sa’o’i kaɗan bayan ficewar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso daga ADC zuwa sabuwar jam’iyyar NDC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.