Ministan Tinubu Ya Tona Yadda Gwamnatin Buhari Ta ‘Saida’ Man Shekaru Masu Zuwa

Ministan Tinubu Ya Tona Yadda Gwamnatin Buhari Ta ‘Saida’ Man Shekaru Masu Zuwa

  • Abdullahi Tijjani Gwarzo yayi bayanin abubuwan da suka ci karo da su bayan sun karbi gwamnatin tarayya a 2023
  • Karamin Ministan ya koka game da halin tattalin arziki, bai ji dadin yadda aka fara garajen sukar mulkin Bola Tinubu ba
  • T. Gwarzo ya wanke shugaban kasa daga sukar da ake yi masa na kawo yunwa, ya ce Tinubu bai dade da shiga ofis ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Abdullahi Tijjani Gwarzo wanda shi ne karamin ministan harkokin gidaje ya yi bayanin halin da suka tsinci kasa a 2023.

A wata zantawa da aka yi da shi, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya nuna abubuwa sun damalmale kafin Bola Tinubu ya shiga ofis.

Tinubu
Karamin ministan gidaje a mulkin Bola Tinubu Hoto: worksandhousing.gov.ng/@Dolusegun16
Asali: UGC

Bayanin ministan ya fito ne daga shafin Gandujiyya Online na Facebook saboda zargin ‘yan adawa sun juya kalaman da ya yi.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga kalaman wakilin na jihar Kano a FEC ne aka fahimi kudin da ake samu daga danyen mai a gwamnati mai-ci ya ragu sosai.

A wani hali Tinubu ya karbi kasa?

"An saida man shekaru biyu tun kafin a hako, sai dai ayi ta addu’a. In ba da taimakon Allah ba, idan an kira mutumin Najeriya, ya amsa?"
"Ba ka jin yadda duniyar ta ke? Saboda haka mutane abin da mu ke bukata, a taimakawa Bawan Allah (Bola Tinubu) nan da addu’a."

- Abdullahi Tijjani Gwarzo

Tinubu bai nufin kowa sai da alheri

Tsohon mataimakin gwamnan na Kano a lokacin Ibrahim Shekarau ya ce shugaba Bola Tinubu yana da manufar alheri ga kasa a rai.

A matsayin Tinubu na kwararren ‘dan siyasa, T. Gwarzo yake cewa shugaban Najeriyan ba zai yi abin da zai cutar da wani ba.

Kara karanta wannan

Aiki na Kyau: Dalilin Shugaba Tinubu na ware Abba, ya jinjina masa cikin Gwamnoni

Minista yana so a kara hakuri da APC

"A kuma taimaka masa da hakuri, bature ya ce ‘he means well’ (yana da manufar alheri), da kyakkyawar fata ga mutanen Najeriya."
Duk wanda zai fito ya soke shi (Bola Tinubu) a yanzu; Yunwa! Yunwa! Yunwa! Yau watan shi nawa? Shi ya kawo yunwa a Najeriya?

- Abdullahi Tijjani Gwarzo

Kamar Buhari, a kyale Tinubu ya yi shekaru 8

Gwarzo yana ganin a yadda ake tafiya, bai dace a fara yi wa gwamnati adawa tun yanzu ba, ya ce kyau mutanen Kudu su more mulki.

Tun da Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas a ofis, yana so a bar Tinubu ya yi hakan, ya zargi abokan adawa da zuga ‘yan Najeriya.

ASUU za su tada hankalin Tinubu

Kamar yadda labari ya gabata, malaman jami’o’i sun bi sahun kungiyoyin kwadago, za su fara wasa wukar tafiya yajin-aiki a kasar nan.

Kara karanta wannan

Muhimman matakai 6 da aka dauka da Tinubu ya zauna da Gwamnoni a Aso Villa

Shugaban ASUU ya ce gwamnatin tarayya ta saba alkawura da ta yi. Har yanzu ASUU tana bin bashin albashin watanni da aka hana ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel