Abubakar Malami: Shari'ar Tsohon Ministan Buhari Ta Dauki Sabon Salo a Kotu

Abubakar Malami: Shari'ar Tsohon Ministan Buhari Ta Dauki Sabon Salo a Kotu

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya na ci gaba da shari'a da tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami kan wasu zarge-zarge
  • A yayin zaman kotu na ranar Laraba, 15 ga watan Afirilun 2026, masu shigar da kara sun gabatar da sabuwar bukata
  • Masu shigar da karar sun yi gyare-gyare kan tuhume-tuhumen da ake yi wa Abubakar Malami SAN da dansa

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi gyara ga tuhume-tuhumen da take yi wa tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami da ɗansa Abdulaziz.

Gwamnatin ta cire zargin da ya shafi ɗaukar nauyin ta’addanci da take yi a baya kan tsohon Ministan na shari'a.

DSS ta gurfanar da Malami a kotu
Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami a kotu Hoto: @OfficialEFCCNg
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa gwamnatin ta yi gyara kan tuhume-tuhumen ne yayin zaman kotu na ranar Laraba, 15 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Dalilin kotun Kaduna na sake 'dage shari'ar neman belin Nasir El Rufa'i

DSS ta yi gyara a tuhumar Abubakar Malami

Lauyan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Akinlolu Kehinde, ya sanar da kotun game da gyaran kuma ya nemi a sauya tsohuwar tuhumar.

Tuhumar da aka gyara ta ta’allaka ne kan mallakar makamai ba bisa ƙa'ida ba.

Shaibu Aruwa, lauyan waɗanda ake ƙara, ya tabbatar da cewa an ba waɗanda yake karewa takardar gyaran tuhumar kuma ya amince da a karanta sabuwar tuhumar ga waɗanda ake ƙara.

Sakamakon haka, aka karanta tuhumar da aka gyara ga waɗanda ake ƙara, inda suka bayyana cewa ba su da laifi, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Ya batun belin Malami da dansa?

Alkalin kotun, mai shari'a Joyce Abdulmalik, ta amince waɗanda ake ƙarar su ci gaba da zama a kan sharuddan belin da aka ba su a ranar 27 ga Fabrairu.

An ɗage shari'ar zuwa ranar 26 ga Mayu da kuma 15 ga Yunin 2026 domin fara sauraron ƙarar.

A cikin tuhumar da aka gyara, masu shigar da ƙara suna zargin cewa an samu makamai da harsasai a gidan Abubakar Malami da ke Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan

"Tinubu na yi wa dimokuradiyya shakar mutuwa": Obi ya ce da matsala gabanin 2027

DSS ta yi gyara a tuhumar da ake yi wa Malami
Abubakar Malami zaune a cikin kotu Hoto: @OfficialEFCCNg
Source: Twitter

DSS ta gurfanar da Malami a kotu

Hukumar DSS ce ta fara gurfanar da Malami da Abdulaziz a ranar 3 ga Fabrairu 2026 a kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin ɗaukar nauyin ta’addanci da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar DSS ta zargi Malami da ƙin gurfanar da masu ɗaukar nauyin ta’addanci waɗanda aka ce an aika wa ofishin babban lauyan gwamnati takardunsu domin gurfanar da su.

A ranar 27 ga Fabrairu, tsohon AGF ɗin da ɗansa sun samu belin Naira miliyan 200 kowannensu tare da mutane biyu da za su tsaya masu.

Jami'an EFCC sun kai samame gidan Malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC sun kai samame gidan Abubakar Malami.

Jami'an na EFCC sun kai samame a gidan tsohon Ministan shari’a da ke Maitama a Abuja domin kwace kadararsa.

Jami’an na EFCC karkashin jagorancin Folarin Sunday Dare, sun isa gidan da kusan motoci biyar, sanye da rigunan aikinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng