Abin da ya jawowa Mustafa Sule Lamido shan kasa a zaben 2019

Abin da ya jawowa Mustafa Sule Lamido shan kasa a zaben 2019

Masana masu bibiyar harkar siyasa su na cigaba da yin tanbihi game da zaben da aka yi a bana. Daily Trust tace daga cikin abin da ya ba jama’a mamaki shi ne yadda Mustapha Lamido ya rasa takarar Sanata.

Daya daga cikin ‘Ya ‘yan tsohon gwamnan Jigawa watau Mustapha Sule Lamido ya nemi kujerar Sanatan Jigawa ta tsakiya a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, amma ya sha kasa a hannun ‘Dan takarar jam’iyyar APC.

Santurakin na Dutse ya rasa zabe ne a dalilin tsoron gujewa zaben shugaba Muhammadu Buhari da mutane su kayi. Jama’a da-dama sun ta zaben jam’iyyar APC ne a yankin Jigawa ta tsakiya saboda farin jinin shugaba Buhari.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa APC ta doke PDP war-was a zaben Legas

Abin da ya jawowa Mustafa Sule Lamido shan kasa a zaben 2019
Alhaji Mustafa Sule Lamido yayi takarar Sanata a zaben 2019
Asali: UGC

Karfin APC sak yana daga cikin abin da ya sa jam’iyyar PDP ta sha kasa a zaben, a dalilin tsoron yin kuskuren zaben PDP a kujerar shugaban kasa. Girman takardar kada kuri’ar ya kuma jawowa Lamido na PDP faduwa zabe.

Haka kuma sauyin-shekar da aka rika yi daga jam’iyyar PDP yayi sanadiyyar doke Mustapha Lamido. Haka kuma tsohon gwamna Sule Lamido, ya cire hannun sa daga takarar ‘Dan na sa, inda yace ba shi ya aike sa takara ba.

Lamido yayi namijin kokari wajen yakin neman zabe inda ya tare da yin kamfe a Kauyuka. A wancan lokaci dai sai da mutane su ka dauka cewa Abokin takarar na sa watau Sabo Nakudu ba zai kai ko ina ba, amma aka ji akasin haka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng