Digirin Bogi: An Nemi Ministan Tinubu Ya Yi Murabus, Ya Mika Kansa ga Hukuma

Digirin Bogi: An Nemi Ministan Tinubu Ya Yi Murabus, Ya Mika Kansa ga Hukuma

  • Kungiyoyi sun fara taso Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji kan zarginsa da amfani da takardun digiri da NYSC na bogi
  • Kungiyar GGSMD ta bukaci Ministan ya yi murabus daga mukamin nan take saboda da takardun karya ya yi amfani wajen nadinsa
  • Ta kuma bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakin gaggawa domin tsaftace gwamnatinsa daga marasa gaskiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kungiyar Global Gender Safety and Moral Development (GGSMD) ta bukaci Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya yi murabus nan take.

Kungiyar ta nemi ministan ya ajiye aiki ne bisa zargin karya a takardun karatu da ya gabatar lokacin nadinsa a mukamin.

Ministan Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Nnaji.
Hoton Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji a ofis a Abuja. Hoto: @ChiefUcheNnaji
Source: Twitter

Shugaban kungiyar, Godwin Erheriene, ne ya yi wannan kira a taron manema labarai da ya gudanar a ranar Litinin, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Uche Nnaji: Ministan Tinubu da ake zargi da amfani da takardun bogi, ya fito ya yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Minista bai gama digiri ba

Tun watan Yuli 2023 ne ake alakanta Ministan da amfani da takardun bogi, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya zabe shi cikin jerin ministoci 28 na farko da ya tura wa Majalisar Dattawa domin tantancewa.

Tun a wancan lokacin, aka yada labarin cewa Nnaji bai kammala karatun jami’a ba, ballantana ya samu damar yin hidima ga kasa watau NYSC.

An zarge shi da gabatar da takardun bogi ga Shugaban Kasa, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Hukumar Tsaro ta DSS da Majalisar Dattawa.

Wani bincike na tsawon shekaru biyu da aka gudanar ya tabbatar cewa Nnaji na amfani sa takardar shaidar digiri daga Jami’ar Nsukka (UNN) da shaidar kammala NYSC na bogi.

GGSMD ta bukaci Nnaji ya yi murabus

Da yake jawabi a taron manema labarai, Erheriene ya bukaci Ministan ya sauka daga mukaminsa, sannan ya mika kansa ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

An bazo wa Minista wuta, Hadimin Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya tsige shi nan take

Shugaban kungiyar ya ce:

“Don kare mutunci da tabbatar da manufar gwamnatin Shugaba Tinubu na yaki da rashawa, kungiyar GGSMD tana kira ga Ministan Kimiyya, Kirkire-Kirkire da Fasaha da ya yi murabus nan take.
"Ya mika kansa ga hukumomin tsaro don a binciki takardunsa cikin gaskiya da adalci, ya kuma bada hadin kai wajen tantancewa. Bai kamata ya shiga kotu yana bata lokaci da kudi wajen kare abin da ya san karya ne ba."

GGSMD ta yi barazanar zanga-zanga

Kungiyar ta kuma yi barazanar yin zanga-zanga a ma’aikatar Kimiyya da Fasaha idan Ministan ya ki sauka daga mukaminsa.

"Idan ba a dauki matakan da suka dace ba, GGSMD za ta yi amfani da hakkinta na doka wajen gudanar da zanga-zanga a Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha domin tilasta daukar matakin ladabtarwa,” in ji kungiyar.
Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji.
Hoton Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji a ofis. Hoto: @chiefuchennaji
Source: UGC

Haka kuma, Erheriene ya soki Hukumar DSS bisa kasa gudanar da cikakken bincike kan takardun Ministan a lokacin tantancewa, cewar rahoton Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

ADC ta tanka zargin da ake yi wa ministan Tinubu na yin amfani da takardun bogi

Ya kuma bukaci Shugaba Tinubu ya dauki lamarin da gaske, yana mai jaddada cewa yakar cin hanci ya shafi kowa a cikin gwamnati.

Hadimin Atiku ya nemi a kori Nnaji

A wani labarin, kun ji cewa Paul Ibe, hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce bai kamata Uche Nnaji ya ci gaba da zama a kujerar Minista ba.

Ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya tsige Ministan nan take tun da Jami'ar UNN ta tabbatar da zargin da ake masa na amfani da digirin bogi.

Paul Ibe ya kara da cewa ya kamata Tinubu ya mika Nnaji ga hukumomin tsaro domin daukar matakin da ya dace a kansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262