Pantami Ya San Makomarsa, APC Ta Tsayar da Dan Takarar Gwamnan Gombe

Pantami Ya San Makomarsa, APC Ta Tsayar da Dan Takarar Gwamnan Gombe

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Gombe ta tsayar da dan takarar gwamnan domin tunkarar zaben shekarar 2027
  • APC ta tsayar da Jamilu Gwamna a matsayin dan takararta na maslaha a zaben shekarar 2027 da ake fuskanta
  • Hakan na nufin tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Ali Pantami, da sauran masu neman takarar gwamna a APC, ba za su samu tikiti ba idan har ba zaben fidda gwani aka yi ba

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Gombe - Jam’iyyar APC a jihar Gombe ta zabi dan takararta na gwamna a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Jam'iyyar APC ta zabi Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta na maslaha domin zaɓen gwamna na shekarar 2027.

APC ta tsayar da dan takarar gwamnan Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya ya daga hannun Jamilu Gwamna Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai darakta janar na fannin yada labaran gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fara samun matsala kan ɗan takara, tsohon shafeta janar zai kara da zabinsa

Jiga-jigan APC sun tsayar da dan takara a Gombe

An cimma wannan matsayar ne ranar Lahadi, 3 ga watan Mayun 2026 yayin wani babban taron masu ruwa da tsaki wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta.

A wurin taron, masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun kuma amince da ’yan takarar maslaha na shiyyoyin sanata guda uku na jihar, kujerun majalisar wakilai guda shida, da kuma mazaɓun majalisar dokoki ta jiha guda 24.

Taron ya samu halartar masu neman takarar Gwamna, na majalisar dokoki ta kasa da na jiha, mambobin kwamitin zartarwa na jiha (EXCO), manyan amintattun jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsaki.

An zabi dan takarar gwamnan APC

Sauran sun hada da mataimakin sakataren kuɗi na APC na kasa, jami’an jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas, da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar.

Zabar ’yan takarar ta hanyar maslaha ya biyo bayan tuntuɓar juna mai faɗi da Gwamna Inuwa Yahaya ya jagoranta, wanda ya haɗa da manyan jiga-jigan jam’iyya, mambobin EXCO, masu neman takara, da masu ruwa da tsaki na matakin gundumomi

Kara karanta wannan

2027: ADC ta saki jadawalin zaben fidda gwani, ta fitar da kudin sayen fom don takara

An yi tuntubar ne da nufin ƙarfafa haɗin kan cikin gida, rage takaddama, da kuma gabatar da tafiya tsintsiya madaurinki ɗaya gabanin zaɓubbuka.

Waɗanda aka amince da su a matsayin ’yan takara a shiyyoyin sanata da na tarayya sun haɗa da: ’

Yan takarar Sanata

  • Gombe ta Tsakiya - DCP Mohammed Ahmadu Deba
  • Gombe ta Kudu - Hon. Jerry Damara
  • Gombe ta Arewa - Muhammadu Inuwa Yahaya

’Yan takarar Majalisar wakilai

  • Mazaɓar Akko - Hon. Usman Bello Kumo
  • Mazaɓar Yamaltu/Deba - Hon. Inuwa Garba
  • Mazaɓar Balanga/Billiri - Hon. Ali Isa JC
  • Mazaɓar Kaltungo/Shongom - Hon. Fatima Binta Bello
  • Mazaɓar Gombe/Kwami/Funakaye - Hon. Saddam Bello
  • Mazaɓar Dukku/Nafada - Hon. Jamilu Shabewa
Jamilu Gwamna ya zama dan takarar gwamnan APC a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya tare da Jamilu Gwamna ana mika masa fom din takara Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Pantami ya kori hadiminsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya kori daya daga cikin hadimansa.

​Farfesa Isa Ali Pantami ya kori hadiminsa bayan wajen bayan ya wallafa kalaman ɓatanci ga abokan hamayya.

Pantami ya bayyana cewa an wallafa saƙon ne ba tare da saninsa ba, inda aka siffanta duk wanda ba ya goyon bayansa, ciki har da malamai, a matsayin munafukai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com